"Shinkafa Ta Dawo N40,000" Gwamnatin Tinubu Ta Aika Sako ga Masu Shirin Zanga Zanga
- Gwamnatin tarayya karkashin Bola Tinubu ta fara share hawayen matasa game da tsadar rayuwa gabanin fara zanga zanga
- Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris ya ce babu sauran buƙatar zanga-zanga domin gwamnati ta fara magance damuwar matasa
- Mohammed ya yi ikirarin cewa an saki buhunan shinkafa a kasuwannni daban-daban kuma ana sayarwa kan farashi N40,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamnatin tarayya karƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta ce babu sauran buƙatar yin zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Najeriya.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris ne ya bayyana haka yayin hira da manema labarai bayan taron majalisar zartaswa..
Ya ce a halin yanzu babu sauran bukatar zanga-zanga domin gwamnati ta fara shawo kan abubuwan da suka damu ƴan Najeriya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Tinubu ta karya farashin shinkafa
Mohammed Idris ya yi ikirarin cewa gwamnatin Tinubu ta magance mafi akasarin koken masu shirya zanga-zanga, inda ya ce an fara sayar da buhun shinkafa a N40,000.
"Galibin koken da masu shirya zanga-zangar nan suka gabatar an magance su, gwamnati na iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin abinci ya wadata."
"Yanzu haka gwamnati ta tura buhunan shinkafa zuwa kasuwanni daban-daban a faɗin ƙasar nan kuma ana siyar da buhu a farashin N40,000. Wannan somin taɓi ne.
"An zuba jari mai dumbin yawa a harkar noma kuma muna ɗa yakinin cewa idan komai ya tafi a haka, farashin kayayyakin abinci zai sauka sosai."
- Mohammed Idris.
Tinubu ya fara biyan buƙatun matasa
Ministan ya ƙara da cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi amanna cewa dukkan koken da matasa suka gabatar an fara shawo kansu.
A cewarsa, tsarin bada lamunin karatu zai tabbatar da cewa duk matashin da yake son samun ilimi ya cika burinsa cikin sauƙi.
Har ila yau, Mohammed Idris ya ce da zarar tashoshin zuba gas na CNG sun fara aiki, duka matsalolin sufuri za su kau.
Ƴan sanda sun saɓa da gwamnatin Neja
Kun ji cewa rundunar yan sandan jihar Neja ta tabbatar da cewa wasu matasa sun fito kan tituna ɗauke da kwalaye a titin Kaduna da ke yankin Suleja.
Hakan dai ya saɓawa gwamnatin Muhammad Umar Bago, wadda ta musanta rahoton ɓarkewar zanga-zanga yau Litinin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng