An Maka Bankin CBN Kara Gaban Kotu Kan Manyan Laifuffuka 3, Bayanai Sun Fito
- Ƙungiyar SERAP ta ce ta maka babban bankin Najeriya (CBN) a gaban kotu bisa zargin ɓatan N100bn na yagaggun kuɗi
- SERAP ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, 28 ga watan Yuli, ta hannun mataimakin daraktan ta, Kolawole Oluwadare
- A cewar ƙungiyar, ta shigar da ƙarar ne a gaban babban kotun tarayya da ke birnin Legas a makon da ya gabata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Opebi, Ikeja - Ƙungiyar SERAP ta maka babban bankin Najeriya (CBN) ƙara a bisa zargin gaza yin bayanin inda sama da N100bn na yagaggun kuɗi suka yi.
SERAP ta ce tana kuma ɗaukar matakin shari’a a kan CBN saboda N12bn da aka warewa ofisoshin babban bankin a Abeokuta, jihar Ogun, da kuma Dutse a jihar Jigawa.
TABLE OF CONTENTS
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta sanya a shafinta na X a ranar Lahadi, 28 ga watan Yulin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
CBN ya saɓa doka - SERAP
Wani dalili kuma da ya sa ƙungiyar SERAP ta kai ƙarar CBN a gaban kotu shi ne bashin N3bn da aka ba jihohin Anambra da Enugu.
An shigar da ƙarar mai lamba FHC/L/MSC/441/2024 a makon da ya gabata a babbar kotun tarayya da ke Legas.
A halin yanzu dai, ba a sanya ranar da za a fara sauraron ƙarar ba.
Zarge-zarge 3 da SERAP ke yiwa CBN
- Rashin bayyana inda sama da N100bn na yagaggun kuɗi da waɗanda suka lalace suke.
- N12bn da aka ware wa ofisoshin CBN a Abeokuta da Dutse
- Bashin N3bn da aka ba jihohin Anambra da Enugu
Karanta wasu labaran kan CBN
- Bashin Naira tiriliyan 37: Gwamnan CBN ya fadi ainihin abin da ya jawo tsadar abinci
- CBN ya yi albishirin rage kudin ruwa, watakila a samu sauki bayan korafin Dangote
- Gwamnatin Tinubu ta shirya karbar harajin N425bn daga wajen bankuna
SERAP za ta yi ƙarar gwamnoni
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar da ke rajin bin diddigin ayyukan tattali ta SERAP, ta gargadi gwamnonin jihohi 36 na Najeriya da ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike.
SERAP ta sanar da bukaci gwamnonin kasar da ministan Abuja da su hanzarta mayar da kudaden kananan hukumomi da suka kalmashe
Asali: Legit.ng