JNI Karkashin Sarkin Musulmi Ta Roƙi Alfarma Daga Wurin Masu Shirin Yin Zanga Zanga

JNI Karkashin Sarkin Musulmi Ta Roƙi Alfarma Daga Wurin Masu Shirin Yin Zanga Zanga

  • Jama’atu Nasril Islam (JNI) karkashin Sarkin Musulmi ta roki masu shirin yin zanga-zanga su haƙura su shiga tattaunawa da gwamnati
  • Sakataren JNI na ƙasa, Khalid Aliyu ya bayyana cewa duk da kowa ya san ana cikin kuncin rayuwa amma ba zanga zanga ce mafita ba
  • Ya kafa misali da yadda zanga-zanga ta rikiɗa ta koma tashin hankali a wasu ƙasashe irinsu Libya, Sudan da sauransu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta yi kira ga masu shirya zanga-zanga da gwamnatin tarayya su hau teburin tattauna domin samun maslaha mai ɗorewa.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, Khalid Aliyu, babban sakataren JNI, ya ce ya zama tilas a zauna teburin tattaunawa tun kafin lamarin ya dagule.

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta gamu da cikas, ƙungiyar ƙwada,o. TUC ta bayyana matsayarta

Mai alfarma sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar.
Jama'atu Nasrul Islam ya bukaci masu shirya zanga zanga da gwamnatin Tinubu su nemi masalaha Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Getty Images

Ya ce duk da ‘yan Najeriya na cikin wahalhalu da ƙuncin rayuwa a yanzu amma zanga-zangar da ake shirin yi ba ita ce mafita ba, kamar yadda The Cable ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zanga: JNI ta bayyana mafita

Sakatarwn JNI ya ce:

“Ƙungiyar JNI karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, na kira ga masu shirya zanga-zangar, masu ɗaukar nauyi da masu taimaka musu.
"Da sauran masu ruwa da tsaki da Gwamnatin Tarayyar Najeriya da su gaggauta shiga tattaunawa tun kafin lamarin ya dagule ko ya kai matakin da ba za a iya shawo kansa ba.
"Babu shakka ’yan Najeriya na cikin mawuyacin hali, amma zanga-zangar da ake shirin yi ba ita ce maganin da zai magance matsalar ba.”

JNI ta kafa misali da wasu kasashe

Khalid Aliyu ya ce duniya cike take da labaru marasa daɗi na illolin da zanga-zangar ta haifar kamar a ƙasashen Libya, Syria, Iraq, US, Ukraine, Tunisia, Sudan, da kuma Rasha.

Kara karanta wannan

Rabiu Kwankwaso ya yi magana kan zanga zangar da matasa ke shirin yi a Najeriya

Ya ce zanga-zangar da ta koma tarzoma ta sanya akasarin wadannan kasashe sun shiga cikin yaƙi ko kuma an lalata wani ɓangarensu, Vanguard ta rahoto.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara zage damtse wajen tabbatar da tsaron domin mutane su samu damar zuwa gonakinsu cikin kwanciyar hankali.

TUC ta tsame kanta daga zanga-zanga

A wani rahoton kun ji cewa Ƙungiyar kwadago TUC ta bayyana cewa ba za ta shiga zanga-zangar da ake shirin yi a watan Agusta ba.

Shugaban TUC, Festus Osifo ya ce ba su san wa waye suka shirya zanga-zangar ba kuma babu waɓda ya tuntuɓe su kan batun ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262