Zanga Zanga Ta Gamu da Cikas, Kungiyar Kwadago, TUC Ta Bayyana Matsayarta

Zanga Zanga Ta Gamu da Cikas, Kungiyar Kwadago, TUC Ta Bayyana Matsayarta

  • Ƙungiyar kwadago TUC ta bayyana cewa ba za ta shiga zanga-zangar da ake shirin yi a watan Agusta ba
  • Shugaban TUC, Festus Osifo ya ce ba su san wa waye suka shirya zanga-zangar ba kuma babu waɓda ya tuntuɓe su kan batun ba
  • Duk da haka Osifo ya yi kira ga sufetan ƴan sanda na kasa ya tabbatar da bada kariya da tsaro ga masu yin zanga-zanga

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Festus Osifo, shugaban kungiyar 'yan kasuwa (TUC), ya ce ƴaƴan kungiyar kwadagon ba za su shiga zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar nan ba.

Rahotanni sun nuna matasan Najeriya sun shirya fita zanga-zangar lumana daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta domin nuna fushinsu kan tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

JNI ƙarkashin Sarkin Musulmi ta roƙi alfarma daga wurin masu shirin yin zanga zanga

Shugaban TUC, Festus Osifo.
Kungiyar kwadago TUC ta tsame kanta daga zanga-zangar da ake shirin yi Hoto: Festus Osifo
Asali: UGC

TUC ta tsame hannu daga zanga-zanga

Da yake jawabi a Abuja ranar Alhamis, Osifo ya ce masu shirya zanga-zangar ba su sanar da ƙungiyar kwadago ta TUC a hukumance ba, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Idan kuka shirya yin zanga-zanga, akwai bukatar ku zauna, ku tattauna kana ku yi tsare-tsare, to amma har zuwa yau babu wanda ya tuntuɓe mu kan zanga-zanga.
"Babu wanda ya sanar da mu cewa ana bukatar haɗin kan mu a wurin wannan zanga-zanda, To, ta yaya kuke tsammanin mu shiga zanga-zangar da ba mu san wanda ke shirya ta ba?
"Ba mu san abin da zai biyo baya ba kuma a matsayin mu na ƙungiya, mu na da rassa da ƙawayen da muka saba tafiyar da al'amuran mu tare."

- Festus Osifo.

TUC ta aika sako ga sufetan ƴan sanda

Kara karanta wannan

Gwamna ya ɗauki matakin hana zanga zangar da ake shirin yi, ya aika muhimmin saƙo

Duk da ba zai fito ba shugaban TUC ya bukaci babban sufeton ‘yan sanda (IGP) da ya tabbatar da cewa an ba masu zanga-zangar tsaro kamar yadda dokar ‘yan sanda ta tanada.

Ya ƙara da cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba ƴan ƙasa damar yin zanga-zanga kuma dokar rundunar ƴan sanda ta tanadi a baiwa masu yi kariya da tsaro, Arise tv ta rahoto.

Kwankwaso ya magantu kan zanga-zanga

A wani rahoton kuma Kwankwaso ya roƙi masu shirya zanga-zanga sun duba sakamakon da zai biyo baya kamar asarar rayuka da dukiyoyi

Jagoran NNPP na ƙasa ya roƙi ƴan Najeriya su yi amfani da ƙarfin kuri'unsu wajen sauya duk shugaban da ya masu ba daidai ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262