Gwamna Ya Yi Watsi da Batun Zanga Zanga, Ya Fadi Matakan da Ya Dauka

Gwamna Ya Yi Watsi da Batun Zanga Zanga, Ya Fadi Matakan da Ya Dauka

  • Gwamnatin jihar Sokoto ta ƙudiri aniyar ƙin shiga zanga-zangar da aka shirya kan halin ƙunci a faɗin ƙasar nan
  • Gwamnatin ta cimma wannan matsayar ne a wani zama da ta yi da masu ruwa da tsaki a jihar a ranar Juma'a, 26 ga watan Yulin 2024
  • Gwamnan jihar, Ahmed Aliyu Sokoto ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na yin haɗin gwiwa da ɓangarorin da abin ya shafa domin samar da zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto ta ƙudiri aniyar ƙin shiga zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a faɗin ƙasar nan.

An ɗauki matakin ne a zaman tattaunawa na masu ruwa da tsaki wanda ya samu halartar shugabannin ƙungiyoyin siyasa da na addini da na ɗalibai da kuma shugabannin ƙwadago.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Kashim Shettima ya ba 'yan Najeriya mafita maimakon yin zanga-zanga

Gwamnatin Sokoto ba za ta shiga zanga-zanga ba
Gwamnatin Sokoto ba ruwanta da zanga-zangar da za a yi Hoto: Ahmed Aliyu
Asali: Facebook

An gudanar da zaman ne a ranar Juma'a, 26 ga watan Yulin 2024, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana matsayarsu, inda ya ce mahalarta taron sun yanke shawarar kada su shiga zanga-zangar saboda “ba ta da amfani”, rahoton New Telegraph ya tabbatar.

Gwamnan ya nuna damuwarsa kan halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan na taɓarɓarewar tattalin arziƙi, hauhawar farashin kayayyaki, da rashin tsaro.

Gwamna Ahmed ya ɗauki matakan rage raɗaɗi

Ya bayyana wasu daga cikin matakan da gwamnatinsa ta ɓullo da su domin taimakawa wajen rage raɗaɗin wahalhalu da suka haɗa da, biyan albashi duk wata a ranar 19 ga wata.

Sauran su ne raba kayan abinci, rabon takin zamani, bayar da kyautar kuɗi a lokutan bukukuwa da dai sauransu.

Gwamnatin jihar ta kuma jaddada ƙudirinta na yin hadin gwiwa da dukkanim bangarorin da abin ya shafa domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Shugaba Tinubu ya sanya labule da gwamnonin APC, an samu bayanai

Gwamna Ahmed Aliyu ya kuma ce yana da ƙwarin gwiwar cewa matakan da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ɗauka za su fitar da ƙasar nan daga cikin ƙalubalen da take fuskanta.

Matsayar mahalarta taron kan zanga-zanga

Wakilan ƙungiyoyin addinai daban-daban, na ƙwadago, da ɗaliban da suka yi jawabi a yayin taron sun tabbatarwa gwamnan cewa mambobinsu ba za su shiga zanga-zangar ba saboda ta saɓawa addininsu da al’adarsu.

Karanta wasu labaran kan zanga-zanga

Ƴan majalisa sun magantu kan zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan majalisar wakilai daga yankin Arewa maso Yamma sun tofa albarkacin bakinsu kan zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a faɗin ƙasar nan.

Ƴan majalisar sun buƙaci al’ummar yankin da kada su shiga zanga-zangar wacce aka shirya fara gudanarwa a ranar, 1 ga watan Agustan 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng