Gwamna Ya Ɗauki Matakin Hana Zanga Zangar da Ake Shirin Yi, Ya Aika Muhimmin Sako
- Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya fara ɗaukar matakai da nufin hana zanga-zangar da ake shirin yi a watan Agusta mai zuwa
- Sanata Uba Sani ya gana da shugabannin hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya, su roki su wayar kan mutane kan illar zanga-zanga
- Ya ce masu shirya wannan zanga zanga suna da wata ɓoyayyar manufa ta tayar da tarzoma da gurgunta kasuwancin ƴan ƙasa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya gana da shugabannin hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya kan zanga-zangar da ake shirin yi.
Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne yayin da matasa ke shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin kasar nan kan tsadar rayuwa da yunwar da ake ciki.
Dalilin ganawar Uba Sani da shugabanni
Taron dai an yi shi ne domin inganta tsaro a manyan yankunan Kaduna da kuma wayar da kan mutane game illar yin zanga-zangar da za a yi, Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Uba Sani ne ya jagoranci taron wanda ya gudana a gidan gwamnati Sir Kashim Ibrahim da ke cikin birnin Kaduna ranar Jumu'a.
Uba Sani ya caccaki masu shirya zanga-zangar inda ya ce duk da ba a san fuskokin su ba amma alamu sun nuna suna ƙoƙarin tayar da tarzoma ne a ƙasar nan.
Ya kuma yi zargin cewa an shirya zanga-zangar ne da nufin cimma wata manufar siyasa da tada hankalin al'umma don sace masu kayan sana'o'insu.
Wace matsaya Uba Sani ya ɗauka?
Ya kuma sha alwashin cewa gwamnatin jihar Kaduna da al’umma ba za su goyi bayan duk wata zanga-zangar da manufarta ita ce tada rikici da cutar da jama’a ba.
A cewar gwamnan, babu buƙatar wannan zanga-zangar da ake shirin yi domin ɓa za ta amfani jihar Kaduna ko ta kawo waraka a Najeriya ba, Tribune Nigeria ta kawo.
Don haka Gwamna Sani ya shawarci sarakuna su wayar da kan jama’arsu kan illolin da ke tattare da shiga zanga-zangar da ka iya tada zaune tsaye a kasar nan.
Ya kuma ba su tabbacin cewa gwamnatin Kaduna ba za ta yi ƙasa a guiwa ba a ƙoƙaren share hawayen al'ummarta musamman saboda halin kuncin da aka shiga.
Yan sanda sun bada damar zanga-zanga
A wani rahoton kuma Rundunar 'yan sanda a Najeriya ta ba matasa masu shirin zanga-zanga damar gudanar da ita cikin lumana ba tare da matsala ba.
Rundunar ta bukaci duka kungiyoyin da ke cikin zanga-zangar su ba da bayansu da na shugabanninsu a hukumance.
Asali: Legit.ng