Zanga Zanga: Kungiyar Matasan Najeriya ta Tura Sako Zuwa ga Rassanta 104

Zanga Zanga: Kungiyar Matasan Najeriya ta Tura Sako Zuwa ga Rassanta 104

  • Kungiyar matasan Najeriya ta National Youth Council of Nigeria (NYCN) bayyana damuwa dangane da halin da 'yan kasa su ka tsinci kansu na kunci
  • Shugaban kungiyar na kasa, Sukubo Sara-Igbe Sukubo ne ya bayyana damuwarsu bayan taron gaggawa da su ka gudanar ranar Alhamis
  • Ya umarci rassanta 104 da ke jihohin kasar nan 36 da su jira umarni na gaba wanda za a sanar a karshen watan Yuli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Kungiyar matasan kasar nan ta National Youth Council of Nigeria (NYCN) ta bayyana rashin jin dadi a kan yadda 'yan kasar nan ke cikin wahala yayin da ake shirin zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Hedkwatar tsaro ta jero mutanen da ake shirin kai wa hari a lokacin zanga zanga

Wannan na zuwa a lokacin da kasar ta kasa zaune ta kasa tsaye saboda batun zanga-zanga da 'yan kasa su ka ce sai sun gudanar a watan Agusta mai kamawa.

Amb Sukubo Saraigbe Sukubo
Kungiyar matasa za ta fadi matsayarta a kan zanga-zanga Horo: Amb Sukubo Saraigbe Sukubo
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Sukubo Sara Igbe Sukubo ya gana da sauran shugabannin kungiyoyin matasa da jiha a kan batun zanga-zanga da sauran natsalolin da su ka shafi kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zanga: Matasa za su bayyana matsayarsu

Kungiyar matasa ta NYCN ta bayyana cewa za ta fadi matsayarta a kan tafiya a kan zanga-zangar gama gari a karshen watan Yuli, Leadership ta wallafa.

Shugaban kungiyar, Sukubo Sara Igbe ne ya bayyana haka, inda ya ce za su fitar da matsayarsu a taron da za su gudanar ranar Laraba 31 Yuli, 2024.

Ya ce taronsu na yau Alhamis ya tattauna da shugabannin kungiyar a jihohi, inda aka zanta a kan tsadar rayuwa da bukatar daukar matakin da ya kamata.

Kara karanta wannan

"Ba mu san dalilinku ba:" Gwamnonin APC sun tura sako ga matasa kan zanga-zanga

An shawarci matasa a kan zanga-zanga

A baya mun ruwaito cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a shekarar 2019, Faduri Oluwadare Joseph ya goyi bayan zanga-zanga da ake shirin yi daga farkon Agusta zuwa 10 Agusta, 2024.

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya bayyana cewa amma dole sai matasa sun sa ido sosai saboda gujewa kutsen bata-gari da ka iya tayar da tarzoma da ka iya jawo asarar rayuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.