Hukumar DSS Ta Gano Masu Shirya Zanga Zanga, Ta Yi Gargadi Mai Zafi

Hukumar DSS Ta Gano Masu Shirya Zanga Zanga, Ta Yi Gargadi Mai Zafi

  • Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) ta ce ta gano masu shirya zanga-zangar adawa da halin ƙuncin da ake ciki a faɗin Najeriya
  • Hukumar DSS a cikin wata sanarwa ta gargaɗi masu shirya zanga-zangar da su yi watsi da shirinsu domin baya da amfani ga ƙasar nan
  • Ta bayyana cewa manufar masu shirya zanga-zangar ita ce kifar da gwamnati musamman gwamnatin tarayya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) ta yi gargaɗi kan zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a faɗin ƙasar nan.

Ana shirya zanga-zangar ne domin nuna adawa da halin ƙunci da wahalhalun da ake fama da su a ƙasar nan.

DSS ta yi gargadi kan zanga-zanga
Hukumar DSS ta gano masu shirya zanga-zanga Hoto: @OfficialDSSNig
Asali: Twitter

DSS ta gano masu ɗaukar nauyin zanga-zanga

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi tuni kan haramcin gudanar da zanga zanga a jihar Arewa

Hukumar ta ce tuni ta gano masu ɗaukar nauyin gudanar da zanga-zangar sannan ta gargaɗe su da kada su gudanar da ita domin hakan ba shi da amfani ga Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gargaɗin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a na hukumar DSS, Dakta Peter Afunanya ya sanya wa hannu, wacce jaridar Vanguard ta samu.

Wane gargaɗi DSS ta yi?

Hukumar ta yi gargaɗin cewa tana da bayanan sirri kan cewa bara-gurbi za su yi kutse cikin zanga-zangar domin kawo hargitsi da tashin hankali a ƙasar nan.

Sanarwar ta yi zargin cewa manufar masu shirya zanga-zanga ita ce sauya gwamnati, musamman kujerar shugaban ƙasa, rahoton Daily Post ya tabbatar.

"Hukumar DSS ta gano masu turo kuɗaɗe, masu ɗaukar nauyi da waɗanda ake haɗa baki da su domin zanga-zangar."
"Sai dai, a matakin yanzu ba amfani da ƙarfin tuwo ba ne ya kamata ayi domin magance matsalar."

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Jigon APC ya fadi abin da 'yan Najeriya ya kamata su yi wa Tinubu

"A maimakon hakan hukumar ta yi amfani da hanyoyin neman maslaha cikin ruwan sanyi da suka haɗa da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin shawo kan mutanen su yi watsi da manufar da suke son cimmawa mara kyau."
"A bisa ga hakan, hukumar na gargaɗin duk ƙungiyoyin zanga-zangar da su yi watsi da duk wani nau'in nuna fushi ko tayar da rigima."

- Peter Afunanya

Karanta wasu labaran kan zanga-zanga

Ƴan sanda sun yi gargaɗi kan zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Borno ta gargaɗi mutanen jihar da su guji shiga zanga-zangar da ake shirin yi a faɗin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Hedkwatar tsaro ta jero mutanen da ake shirin kai wa hari a lokacin zanga zanga

Rundunar ta bayyana cewa dokar ta ɓaci kan rashin tsaro da ke ci gaba da aiki a Borno kai tsaye ta haramta gudanar da zanga-zanga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng