Gwamnati Ta Bayyana Jihar Arewa da Ba Za a Gudanar da Zanga Zanga Ba

Gwamnati Ta Bayyana Jihar Arewa da Ba Za a Gudanar da Zanga Zanga Ba

  • Gwamnatin jihar Bauchi ta fito ta bayyana matsayarta kan zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a faɗin ƙasar nan
  • Sakataren gwamnatin jihar, Barista Ibrahim Kashim, ya bayyana cewa babu wata zanga-zanga da za a gudanar a Bauchi
  • Ya ja kunnen masu shirin gudanar da zanga-zangar da su tafi wani waje can daban ba jihar ba, idan har sai sun yi zanga-zangar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana cewa ba za a yi zanga-zanga a jihar ta yankin Arewa maso Gabas ba.

Gwamnatin ta kuma gargaɗi masu shirin gudanar da zanga-zangar da su shiga taitayinsu sannan su sake tunani.

Gwamnatin Bauchi ta ce ba zanga-zanga a jihar
Gwamnatin Bauchi ta ce ba za a yi zanga-zanga a jihar ba Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed
Asali: Facebook

Babu batun zanga-zanga a Bauchi

Sakataren gwamnatin jihar, Barista Ibrahim Kashim, ya bayyana hakan ga manema labarai lokacin da yake tsokaci kan zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a ƙasar nan, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

"Mun gano wata maƙarƙashiya," Sojoji sun aika saƙo ga masu shirin yin zanga zanga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barista Ibrahim ya kuma yi watsi da raɗe-raɗen cewa za a gudanar da zanga-zangar a cikin jihar, rahoton tashar AIT ya tabbatar.

Ya nuna cewa jihar ta yi suna wajen zaman lafiya da kwanciyar hankali saboda haka ba za su yi maraba da abin da zai kawo cikas ga hakan ba.

Wane gargaɗi gwamnatin ta yi?

Sakataren gwamnatin na jihar Bauchi ya kuma ja kunnen masu zanga-zangar da su gudanar da ita a wani waje daban ba a jihar ba idan sun dage cewa sai sun yi ta.

"A ɓangaren gwamnati, mun nesanta kanmu daga kowace irin zanga-zanga. Ba mu da masaniya, ba mu yin maraba da kowace irin zanga-zanga sannan kuma ba za ta faru a jihar Bauchi ba."
"Idan har sun haƙiƙance kan cewa sai sun yi zanga-zangar, sai su je su yi a wani waje daban ba a jihar Bauchi ba."

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya tsure, ya bayyana fargabarsa a kan shirin zanga zangar lumana

- Barista Ibrahim Kashim

Gwamnoni sun yi magana kan zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta yi magana kan al'amuran tsaro musamman zanga-zangar da matasa ke shirin yi a watan Agusta.

Ƙungiyar ta bayyana cewa bayanan da ta samu daga ofishin mai bada shawara kan harkokin tsaron ƙasa (NSA) sun nuna damuwar da ake ciki game da zanga-zangar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng