Dangote: Ƴan Majalisa Sun Fusata, Sun Buƙaci Tinubu Ya Dakatar da Shugaban NMDPRA
- 'Yan majalisar wakilai sun baukaci shugaba Bola Tinubu da ya dakatar da shugaban NMDPRA kan rikicinsa da Aliko Dangote
- 'Yan majalisar sun ce duk zarge-zargen da yayi babu gaskiya a ciki domin a gabansu an yi gwajin dizal ɗin matatar Dangoten
- Sun zargi Farouk Ahmed da rashin iya aiki tare da zagon ƙasa ga matatar cikin gida yayin da suke bada lasisin shigo da dizal mara kyau
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Majalisar wakilai ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya dakatar da shugaban NMDPRA, Farouk Ahmed kan kalaman da yayi na rashin ingancin dizal din matatar Dangote.
Majalisar ta bauƙaci a dakatar Farouk Ahmed ne har zuwa lokacin da za a samu sakamakon binciken zarge-zargen da ya yi wa matatar Dangoten.
Majalaisar wakilan ta yi wannan kiran ne yayin amincewa da kudurin buƙatar jama'a wanda ɗan majalisa Esosa Iyawe ya miƙa a zauren ranar Talata, Daily Trust ta bayyana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Dizal din Dangote na da inganci" - Majalisa
A yayin gabatar da kudurin buƙatar, Hon. Iyawe ya bayyana cewa shugaban NMDPRA yi ikirarin cewa dizal ɗin matatar Dangote ba shi da inganci idan aka kwatanta da wanda ake siyowa a ketare.
Sai dai dan majalisar ya ce a ziyarar da suka kai matatar Dangote da kuma gwajin da aka yi wa dizal din matatar da na kasar waje ya nuna akasin ikirarin Farouk.
Hon. Iyawe ya ce:
"A sukar wannan maganar, Dangote ya buƙaci a yi gwaji kan dizal din matatarsa wanda wasu 'yan majalisar wakilai suka je yin gwajin domin tabbatar da hakan.
"Dizal ɗin Dangote yana ƙunshe da sulphur 87.6 ppm, yayin da sauran samfurorin biyu suka ƙunshi sulphur da ya wuce 1800 da 2000 pm, wanda hakan ya ƙaryata iƙirarin shugaban NMDPRA."
Dangote: 'Yan majalisa sun fusata da Farouk
Arise News ta ruwaito cewa, majalisar ta ce shugaban NMDPRA ya yi gaggawar yanke hukunci ba tare da bincike ba tare da furta kalamai masu iya tunzura 'yan kasa.
"An zargi cewa NMDPRA tana ba wa wasu 'yan kasuwa lasisin shigo da dizal mai ƙunshe da sulphur sosai, kuma amfani da shi na kawo haɗurran cutuka.
“Kalaman shugaban NMDPRA, wanda tuni aka ƙaryata, ya janyo cece-kuce daga 'yan Najeriya inda suka zargi zagon-ƙasa ga matatar cikin gida.
"Kalaman shugaban NMDPRA na 'karya' ba tare da bincike ba ya nuna rashin ƙwarewarsa, musamman a yayin da ake tsaka da yunkurin zanga-zanga a fadin ƙasar nan."
- A cewar Esosa Hon. Iyawe.
"Wasu 'yan Najeriya sun fi ni kudi" - Dangote
A wani labari na daban, mun ruwaito muku cewa Alhaji Aliko Dangote, fitaccen attajirin Afrika, ya ce ba shi ke juya kasuwa a Najeriya ba.
Ya bayyana cewa akwai wadanda suka fi shi tsabar kudi a Najeriya kuma yana gayyatarsu da su hanzarta narka su wurin saka hannayen jari a gida.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng