Shugaban Majalisa Ya Nemi Afuwar Sanata Bayan Ya Fuskanci Matsin Lamba
- Bayan fuskantar suka daga wajen ƴan Najeriya, shugaban majalisar dattawa ya nemi afuwar takwararsa, Natasha Akpoti-Uduaghan
- Sanata Godswill Akpabio a yayin zaman majalisar na ranar Talata, ya bayyana cewa yana ganin ƙima tare da mutunta mata
- Shugaban na majalisar dattawan dai ya nemi afuwar ne bayan a kwanakin baya ya ce mata majalisar ba gidan rawa ba ne
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya nemi afuwar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Godswill Akpabio ya nemi afuwar Sanatan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, kan wasu kalamai da ya furta mata a kwanakin baya.
Ƴan Najeriga sun caccaki Akpabio
Sanata Akpabio dai ya gayawa Natasha cewa majalisar ba gidan rawa ba ne domin haka sai an ba ta izni kafin ta yi magana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalaman na shugaban majalisar dai sun jawo ya sha suka sosai a wajen ƴan Najeriya.
Amma da yake jawabi a ranar Talata, 23 ga watan Yuli, yayin zaman majalisar, Akpabio ya ce ba zai taɓa wulaƙanta mace da gangan ba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Akpabio ya nemi afuwar Sanata Natasha
Ya kuma nemi afuwar Sanata Natasha sannan ya buƙaci ƴan Najeriya da su bar lamarin ya wuce haka nan, rahoton jaridar The Cable ya tabbatar.
"Na yi matuƙar farin ciki kan yadda ƴan Najeriya suke sanya ido kan abubuwan da suke faruwa a majalisar nan."
"Duba da yadda suke lura da abubuwan da ke faruwa a nan, hakan na nufin cewa muna tare da mutanenmu."
"Amma ba a fahimci abin da na ce ba a wajen gaba ɗaya. Ba zan taɓa ƙasƙantar da wata mace ba, ina da mata da ƴaƴa kuma koda yaushe ina addu'ar Allah ya ɗaga darajar mata."
"Mai girma Sanata Natasha ina mai baki haƙuri."
- Godswill Akpabio
Majalisa ta amince da ƙudirin dokar albashi
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta yi gaggawar amincewa da ƙudirin dokar mafi ƙarancin albashi na ƙasa na shekarar 2019 (wanda aka yiwa kwaskwarima).
Majalisar dattawan ta amince da ƙudirin dokar ne a yayin zamanta na ranar Talata, 23 ga watan Yulin 2024 a birnin tarayya Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng