Jawabin da Ya Ceci Sarkin Gaya, Gwamnan Kano Ya Dawo da Shi da Aka Kirkiro Masarautu

Jawabin da Ya Ceci Sarkin Gaya, Gwamnan Kano Ya Dawo da Shi da Aka Kirkiro Masarautu

  • Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir ya rungumi kaddara, ya ce haka Allah ya nufa da aka ruguza masarautu a watan Mayu
  • Bayan watanni kusan biyu sai ga shi Mai martaba ya dawo kan mulki, gwamnatin jihar Kano ta maida masa rawaninsa
  • Sarkin ya gaji Alhaji Ibrahim Abdulkadir ne wanda ya Dr. Abdullahi Ganduje ya nada kuma ya rasu yana kan karaga a 2021

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Sarkin Gaya yana cikin wadanda suka rasa mulki a lokacin da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta rusa masarautun jihar Kano a Mayu.

Inda Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir ya sha bam-bam da sauran sarakunan shi ne ya rungumi kaddara, ya bar lamarin ga Allah SWT.

Kara karanta wannan

Malami ya kasafta yadda karamin ma’aikaci zai karar da albashin N70, 000 a abinci a wata

Sarkin Gaya
Gwamnan Kano ya dawo da Sarkin Gaya, Aliyu Ibrahim Abdulkadir Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Idan za a tuna, a lokacin da BBC Hausa ta yi hira da Mai martaba Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir, ya nuna bai ji haushin gwamnati ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: Sarkin Gaya bai jin haushin kowa

“Duk wanda hakan ta faru da shi ba zai ji dadi ba. Amma ba mu jin haushin kowa, ba mu jin haushin komai."
"Wani mawaki yana cewa ‘wawa yake fushi da yin Allah’. Wannan yin Allah ne, mun karbe shi hannu biyu-biyu."

- Sarkin Gaya

Gwamna ya yi umarni, Sarkin Gaya ya bi

Kamar yadda ya fada a watan Mayu, gwamnati ta na ba da awanni cewa su bar fadarsu, ya fita tun kafin wa’adin nan ya cika.

Mai Martaban ya ce babu abin da zai kai shi kotu domin yin shari’a da gwamnati domin hakan tamkar ja da Ubangiji SWT ne.

Kara karanta wannan

Kalamai a kan gwamnatin da suka tsumbula Sanata Ndume cikin ruwan zafi a APC da majalisa

A lokacin da gwamnatin Kano ta rushe masarautarsa, Sarkin ya ba al’umma hakuri tare da yin kira a zauna cikin zaman lafiya.

Sarkin Gaya bai je kotu ba

"Dama can da Allah ya ba mu, ai ba kotu mu ka je ba. Kuma idan Allah ya karba sai mu ka je kotu, karar wa mu ka kai kenan?"

The Cable ta rahoto cewa tuni an mika masa takardar dawo da shi kan mulki domin fara aiki.

Sarkin Gaya ba zai rana sarauta ba

Sai dai ko a watan Mayu, Sarkin ya ce idan gwamna ya yi masa tayin sarauta, zai karba a guje.

Basaraken ya ce sun gaji mulki kuma zai sake karban mulki ba tare da la’akari da darajar rawaninsa ba domin ya taimakawa al’umma.

Bayan godiya ga Allah SWT tare da fatan zaman lafiya a Gaya da daukacin jihar Kano, an ji Mai martaba ya roki Allah ya kauda fitina.

Kara karanta wannan

Zargin biyan malamai N16m domin rufe masu baki ya fusata Sheikh Mansur Sokoto

An yi hayaniya saboda tsige Sarakuna

A karshen watan Mayu, an ji labari zanga-zanga ta barke a Gaya da Nasarawa kan mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

Masu zanga-zangar suna kira ne da a tsige Sanusi II tare da mayar da Aminu Ado Bayero wanda ya tare a karamar fada da ke Nassarawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng