Tinubu Zai Shilla Zuwa Kasar Waje Ana Shirin Fara Zanga Zanga

Tinubu Zai Shilla Zuwa Kasar Waje Ana Shirin Fara Zanga Zanga

  • Jirgin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai shilla zuwa ƙasar Ghana mai makwabtaka da Najeriya a ranar Asabar, 20 ga watan Yulin 2024
  • Shugaba Tinubu zai je ƙasar nan domin halartar taron ƙungiyar Tarayyar Afirika (AU) na tsakiyar shekara
  • A matsayinsa na shugaban ƙungiyar ECOWAS, Tinubu zai gabatar rahoto kan halin da ƙungiyar take ciki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu  zai tashi daga Najeriya zuwa ƙasar Ghana a ranar Asabar, 20 ga watan Yulin 2024.

Shugaban ƙasan zai ziyarci ƙasar ne domin halartar taron tsakiyar shekara na ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU).

Tinubu zai ziyarci kasar Ghana
Tinubu zai halarcin taron AU a kasar Ghana Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Mai magana da yawun shugaban ƙasan, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa wacce Dada Olusegun ya sanya a shafinsa na X a ranar Juma'a, 19 ga watan Yulin 2024.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi wa ƴan ƙwadago alƙawari 1 bayan amincewa da albashin N70,000 a Aso Villa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu zai halarci taron AU

Ajuri Ngelale ya ce za a gudanar da taron ne daidai da taken ƙungiyar AU na shekarar 2024, wato ‘Ilimantarwa da ƙarfafa Afirka a ƙarni na 21’.

Ya ce Tinubu, wanda shi ne shugaban kungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS), zai gabatar da rahoton shekarar 2024 kan halin da ƙungiyar ke ciki a wurin taron.

Ya ce rahoton zai ta'allaka ne kan zaman lafiya, tsaro na yanki, shugabanci, tattalin arziki, ayyukan jin ƙai da zamantakewa, makamashi, ma'adanai da noma.

“A matsayinsa na shugaban ƙungiyar ECOWAS, Shugaba Tinubu zai yi jawabi a taron kan matsayin haɗewar yanki a sassa daban-daban na Afirka."
"Zai mayar da hankali kan nasarori da ƙalubalen da aka fuskanta a Yammacin Afirka tun bayan taron ƙarshe a Nairobi, Kenya, a cikin watan Yulin 2023."

- Ajuri Ngelale

Kara karanta wannan

Tinubu ya sanya labule da shugabannin kungiyoyin kwadago, an samu bayanai

Ngelale ya ƙara da cewa Tinubu wanda zai samu rakiyar wasu manyan jami'an gwamnati zai dawo Najeriya bayan kammala taron.

Majalisa ta fara bincike kan tsadar siminti

A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamitin haɗin gwiwa na majalisar wakilai da ke binciken hauhawar farashin siminti a ƙasar nan, ya fara zama da manyan kamfanonin da ke samar da simintin.

Kwamitin ya buƙaci manyan kamfanonin da su gabatar da takardu kan kuɗaɗen da suke kashewa wajen samar da shi wanda ya sanya farashinsa ya tashi a kasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng