Gwamna Zulum Ya Ba 'Yan Najeriya Muhimmiyar Shawara Ana Shirin Fara Zanga Zanga
- Gwamnan jihar Borno, Farfesa Umara Zulum, ya yi kira ga al'ummar jihar da ƴan Najeriya da ka da su yi zanga-zanga
- Gwamnan ya bayyana cewa zanga-zanga ba za ta haifar da wani ɗa mai ido face kawo wahala ga ƴan Najeriya
- Kalaman gwamnan na zuwa ne yayin da ake shirin fara yin zanga-zanga a faɗin ƙasar nan a wata mai zuwa kan tsadar rayuwar da ake ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ba al'ummar Borno da ƴan Najeriya baki ɗaya shawara kan zanga-zangar da ake shirin yi.
Gwamnan na Borno ya buƙace su da su guji shiga zanga-zangar da ake shirin yi a faɗin ƙasar nan a wata mai zuwa.
Gwamna Zulum ya yi wannan roƙon ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki a gidan gwamnatin jihar dake Maiduguri a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace shawara Gwamna Zulum ya ba da?
Ya ci gaba da cewa kamata ya yi jama'a su yi tattaunawa mai ma’ana domin zanga-zangar na iya haifar da tarzoma da ɓarna a ƙasa, rahoton Pulse.ng ya tabbatar.
Ya yi nuni da cewa jihar ta sha fama da matsalar tsaro fiye da shekara 13, inda ya ƙara da cewa zanga-zangar ba za ta kasance hanya mafi inganci domin samun ɗorewar zaman lafiya a jihar ba.
"Duk wani karya doka da oda da za a yi zai zama mummunan abu a gare mu. Ina roƙon jama'a ba na jihar Borno kaɗai ba, amma duka ƴan Najeriya da su guji yin zanga-zanga wacce za ta kawo wahala ga ƴan Najeriya."
"Mu shiga tattaunawa mai ma'ana, gwamnatin tarayya da na jihohi na bakin ƙoƙarinsu domin tabbatar da cewa an samu sauƙin halin matsin da ake ciki a yanzu."
"Gwamnatin jihar Borno da al’ummar jihar sun shafe shekara 13 suna fama da tashe-tashen hankula amma a hankali zaman lafiya ya dawo jihar Borno kuma akwai bukatar mu wanzar da hakan."
- Babagana Umara Zulum
Karanta wasu labaran kan zanga-zanga
- "Ku guji zanga zangar adawa da gwamnati," Sheikh Kabiru Gombe ya shawarci matasa
- "Ba a tada fitina," Sheikh Maqari ya fadi ra'ayinsa kan zanga-zanga a musulunci
- Jerin malaman da suka goyi bayan zanga-zanga da waɗanda suka hana
Sheikh Gumi ya lissafo sharuɗan zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa fitaccen malamin addinin Musuluncin ya ce lallai akwai bukatar al'ummar Najeriya su yi taka tsan-tsan yayin da suka shirya gudanar da zanga-zangar.
Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya ce matasa su gudanar da zanga-zanga amma idan sun cika sharudda shida.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng