Gwamnan Bauchi Ya Kori Wani Babban Jami'i Daga Mukaminsa, Ya Ba Shi Sabon Umarni
- Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya sallami babban mai ba shi shawara kan harkokin tsaro daga kan muƙaminsa
- Gwamna Bala ya kori Ahmed Chiroma ne daga kan muƙaminsa a ranar Talata, 16 ga watan Yulin 2024
- Gwamnan ya umarce shi da ya miƙa ragamar ofishinsa ga babban jami'in tsaro na gwamnan sannan ya gode masa bisa gudunmawar da ya ba jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya amince da korar babban mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Ahmed Chiroma, nan take.
Gwamnan ya amince da sallamar da aka yi wa mai ba shi shawara kan harkokin tsaron ne a ranar Talata, 16 ga watan Yulin 2024.
An kuma umarce shi da ya miƙa ragamar ofishin ga babban jami'in tsaron gwamnan, cewar rahoton jaridar Nigerian Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Bala ya yi kora a Bauchi
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman ga gwamnan kan harkokin yaɗa labarai, Kwamared Mukhtar Gidado, ya fitar, rahoton jaridar Aminiya tabbatar.
Sanarwar na ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Barista Ibrahim Mohammed Kashim.
"Mai girma gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala A. Mohammed CON, Fnipr (Kauran Daular Usmaniya) ya amince da soke naɗin babban mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Ahmed Adamu Chiroma PhD nan take."
"An sanar da shi korarsa daga kan muƙaminsa ta hanyar wata wasiƙa wacce sakataren gwamnatin jiha, Barista Ibrahim Mohammed Kashim ya sanyawa hannu."
"An umarce shi da ya miƙa ragamar ofishinsa ga babban jami'in tsaro na gwamna."
"Gwamna Bala Mohammed a madadin gwamnati da al'ummar jihar Bauchi ya godewa tsohon mai ba da shawara kan tsaron bisa gudunmawar da ya ba jihar Bauchi."
- Kwamared Mukhtar Gidado
Gwamnan Bauchi ya karya farashin taki
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya ƙaddamar da shirin taimakawa manoman jihar da takin zamani a farashi mai rahusa.
Gwamna Bala ya ce gwamnatinsa za ta sayarwa manoma takin zamani na NPK kan farashin N20,00 kan kowane buhu a kan N20,000.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng