Ana Jimamin Rasuwar Jagaban, Wani Ɗan Majalisar Tarayya Daga Kaduna Ya Mutu
- Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Chikun da Kajuru ta jihar kaduna, Hon Ekene Abubakar Adams ya mutu da safiyar ranar Talata
- Rahotanni sun nuna cewa ɗan majalisar wanda ya ci zaɓe a 2023 karkashin LP ya rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya
- Sai dai har kawo yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga majalisar wakilai ta ƙasa kan rasuwar Honorabul Abubakar Adams
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Majalisar wakilan tarayya ta sake shiga jimami yayin da wani 'dan majalisar daga jihar Kaduna ya riga mu gidan gaskiya.
Hon. Ekene Abubakar Adams, mai wakiltar mazaɓar Chikun/Kajuru a majalisar wakilan tarayya ya rasu da sanyin safiyar yau Talata, 16 ga watan Yuli, 2024.
An tabbatar da rasuwar Ekene Adams
Abokin marigayi Adams, Mista Mike Obasi ne ya tabbatar da rasuwar ga jaridar Leadership ta sakon manhajar WhatsApp.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gabanin rasuwarsa, Honorabul Ekene Adams shi ne shugaban kwamitin kula da harkokin wasanni a majalisa ta 10, Daily Trust ta ruwaito.
Mike Obasi ya bayyana cewa Ekene Adams ya rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
Legit Hausa ta tattaro cewa Adams ya zama ɗan majalisa na biyu da ya rasu cikin mako guda biyo bayan mutuwar Hon Olaide Akinremi (Jagaban) daga jihar Oyo.
Akinremi, mai wakiltar mazaɓar Ibadan ta Arewa ya rasu ne ranar Laraba, 10 ga watan Yuli, 2024 yana da shekaru 51 a duniya.
Takaitaccen bayani kan Hon Adams
Marigayin, tsohon kocin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Kada Cuty FC da Remo Stars ya samu nasarar zama mamban majalisar wakilai a 2023 karƙashin inuwar Labour Party.
Duba da gogewarsa a kan harkar wasanni, majalisa ta naɗa shi shugaban kwamitin wasanni, muƙamin da ya rike har zuwa rasuwarsa yau Talata.
Kotu ta sauke ɗan majalisar Sokoto
A wani rahoton kuma Kotun sauraron ƙorafe-korafen zaɓe a jihar Sakkwato ta soke nasarar wani dan majalisar wakilan tarayya Umar Yusuf Sabo.
Ta kuma umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta shirya sabon zaɓe a rumfunan zaɓe huɗu daga nan zuwa kwanaki 90.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng