Shugaba Tinubu Ya Ji Koken Ƴan Najeriya, Ya Bada Tallafin Tirelolin Shinkafa a Jihohi 36

Shugaba Tinubu Ya Ji Koken Ƴan Najeriya, Ya Bada Tallafin Tirelolin Shinkafa a Jihohi 36

  • Yayin da ake fama da yunwa, Gwamnatin Tarayya ta bayar da gudummuwar tirelolin shinkafa ga jihohi 36 da birnin tarayya Abuja
  • Ministan yaɗa labarai, Muhammed Idris ya ce an bada wannan tallafin ne domin rabawa ƴan Najeriya masu karamin karfi
  • Ya ƙara da cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya kudiri aniyar tabbatar da kowane ɗan Najeriya ya samu abincin da zai sa a bakinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta bada tallafin buhunan shinkafa ga jihohi 36 da Abuja domin ragewa ƴan Najeriya raɗaɗi.

Gwamnatin ta sanar da cewa ta bayar da tallafin tirelolin shinkafa 20 ga gwamnoni 36 da birnin tarayya domin rabawa ƴan Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu, ya faɗi mafita a Najeriya

Bola Tinubu.
Gwamnatin tarayya ta bada gudummuwar tirela 20 na shinƙafa ga gwamnoni 36 da Abuja Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Muhammed Idris ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan taron majalisar zartaswa a Aso Villa yau Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce wannan tallafin an ware shi ne ga talakawan Najeriya kaɗai waɗanda ke cikin tsananin buƙata, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Tinubu ya shirya magance yunwa

Muhammed Idiris ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta kudiri aniyar tabbatar da cewa kowane ɗan Najeriya ya samu abincin da zai riƙa kaiwa bakin salati.

Ministan ya ce wannan shi ne mataki na farko yayin da gwamnati ke ƙoƙarin daukar matakan magance matsalar karancin abinci a faɗin ƙasar nan.

Haka nan kuma ya yi kira ga gwamnonin da su tabbatar da an yi adalci wajen rabon wannann kayan abinci domin ya kai ga waɗanda aka yi domin su watau marasa galihu.

Kara karanta wannan

A ƙarshe, Bola Tinubu zai miƙa sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata ga majalisa

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, gwamnatin tarayya ta amince da bai wa jihohin tirelolin shinkafar ne a wurin taron majalisar zartaswa karkashin Bola Tinubu.

Gwamnan Bauchi ya tallafawa manoma

A wani rahoton na daban kun ji cewa yayin da damina ta kankama Gwamna Bala Mohammed ya kaddamar da sabon shirin tallafawa manoma a jihar Bauchi.

Gwamnan ya bayyana cewa shirin zai sayar da takin zamani a kan N20,000 kuma zai samar da sauran kayayyakin noma a farashi mai sauƙi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262