"Dalilin da Ya Sa 'Yancin Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi Ba Zai Yi Aiki Ba" Inji Tsohon Gwamna

"Dalilin da Ya Sa 'Yancin Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi Ba Zai Yi Aiki Ba" Inji Tsohon Gwamna

  • Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi magana kan hukuncin Kotuk Ƙoli kan ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi
  • Fayose ya bayyana cewa majalisun dokoki na jihohi da gwamnoni za su ci gaba da zama ƙarfen ƙafa ga ƙananan hukumomi
  • Ya nuna cewa gwamnatin tarayya da kotun ba za su iya raba ƙananan hukumomi da gwamnoni ba, domin sai da goyon bayan gwamna ake zama shugaban ƙaramar hukuma

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya bayyana damuwarsa kan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke kan ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi.

Jigon na jam’iyyar PDP ya jaddada cewa duk da hukuncin kotun, majalisun dokokin na jihohi da gwamnoni za su ci gaba da kasancewa ƙarfen ƙafa ga cin gashin kan ƙananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta ba gwamnan PDP shawara kan 'yancin kananan hukumomi

Fayose ya magantu kan 'yancin kananan hukumomi
Fayose ya ce gwamnoni za su kawo cikas ga 'yancin cin gashin kan kananan hukumomi Hoto: Ayodele Fayose
Asali: Facebook

Ayo Fayose ya bayyana haka ne a yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' a ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fayose a kan ƴancin ƙananan hukumomi

Jaridar Daily Trust ta ce tsohon gwamnan ya jaddada cewa babu wanda zai iya zama shugaban ƙaramar hukuma ba tare da samun goyon bayan gwamna ba.

Ya jaddada cewa gwamnatin tarayya da kotun ba za su iya 'raba jariri da mahaifiyarsa ba'.

"Yayin da ban yarda wani gwamna ya taɓa kuɗaɗen ƙananan hukumomi ba, bari na gaya maka ƙarara a wannan yammacin cewa ba za a iya raba jariri da mahaifiyarsa ba."
"Babu wanda zai iya zama shugaban ƙaramar hukuma ba tare da taimakon gwamna ba. Duk wanda yake faɗin saɓanin hakan kawai yana ɓata lokacinsa ne."
"Yayin da ba na adawa da hukuncin kotun, amma ta yaya hakan zai zama wani abu mai amfani saɓanin tsarin da ake da shi a yanzu?"

Kara karanta wannan

Daga karshe Gwamna Zulum ya fadi dalilin kai harin kunar bakin wake a Borno

"A yadda abubuwan suke a yau, za a ci gaba da yadda ake yi ne kawai. Ba zai yiwu ina gwamna ka ce mani ba zan iya naɗa wanda nake so ya zama shugaban ƙaramar hukuma ba."

- Ayodele Fayose

Gwamna Makinde ya soki hukuncin kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya yi martani bayan hukuncin Kotun Koli kan ƴancin ƙananan hukumomi.

Gwamna Seyi Makinde ya ce an yi hukuncin ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke cikin wani mawuyacin hali domin ɗauke musu hankali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng