Ba a Gama Jimamin Daliban Plateau Ba, Wani Gini Ya Sake Ruftowa Kan Mutane
- An shiga jimami da firgici a unguwar Sabo da ke birnin Osogbo, babban birnin jihar Osun bayan wani gini ya rufto kan mutane
- Wata majiya ta bayyana cewa ginin ya rufto ne da safiyar ranar Lahadi da misalin ƙarfe 7:30 na safe inda ya danne mutum biyar
- Kakakin hukumar NSCDC ta jihar, ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce an ceto mutum biyu yayin da ake ƙoƙarin ceto sauran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Osun - Wani gini wanda ya zama kango a unguwar Sabo da ke birnin Osogbo, babban birnin jihar Osun ya rufto a ranar Lahadi.
Ruftowar ginin wanda ake zargin ƴan daba na amfani da shi ta sanya mazauna unguwa sun shiga fargaba.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa mutane biyar sun maƙale a cikin ginin wanda ya rufto da misalin ƙarfe 7:30 na safe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattaro cewa ginin wanda bene ne mai hawa biyu da ya zama kango, ƴan daba na amfani da shi a matsayin maɓoyarsu kafin ya rufto.
Yadda gini ya rufto a Osun
Wata majiya mai suna Tunde, ya bayyana cewa ginin mafaka ce a wajen ƴan ƙungiyar asiri, ƴan daba da sauran ɓata gari, sannan jami'an tsaro sun sha kai samame kafin ruftowarsa a ranar Lahadi da safe.
"A yanzu haka da na ke magana, jami'an tsaro da masu aikin ceto sun iso wajen. Sun zo da kayan aiki zuwa wajen, sun ceto mutum uku daga ɓuraguzan."
- Tunde
Me hukumomi suka ce kan lamarin?
Kakakin rundunar sibil difens (NSCDC) ta jihar Osun, Kehinde Adeleke, ta tabbatar da aukuwar lamarin.
Ta bayyana cewa ginin ya rufto ne da safiyar ranar Lahadi, 14 ga watan Yuli da misalin ƙarfe 7:30 na safe inda ya danne mutum biyar.
Kehinde Adeleke ta kuma ƙara da cewa an ceto mutum biyu yayin da sauran mutum uku suka maƙale sannan ana ci gaba da ƙoƙarin ceto su.
Gini ya rufto kan ɗalibai
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗalibai masu yawa sun malale a wata makaranta da ta rufta ana tsakiyar jarabawa a jihar Plateau.
Lamarin ya faru ne a wata makaranta da ke unguwar Busa Buji a ƙaramar hukumar Jos ta jihar Filato a shiyyar Arewa ta Tsakiya.
Asali: Legit.ng