Mutane da Dama Sun Makale Yayin da Gini Ya Rufto Musu a Abuja, An Samu Bayanai

Mutane da Dama Sun Makale Yayin da Gini Ya Rufto Musu a Abuja, An Samu Bayanai

  • An shiga jimami a birnin tarayya Abuja bayan wani bene mai hawa biyu ya rufto kan mutane da safiyar ranar Asabar, 13 ga watan Yulin 2024
  • Mutane da dama ne suka maƙale a ginin wanda a baya asibiti ne a wajen kafin a mayar da shi gidan zama
  • An garzaya da wasu mutum biyu zuwa asibiti domin duba lafiyarsu bayan masu ba da agajin gaggawa da jami'an tsaro sun hallara zuwa wajen da lamarin ya auku

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wani sashe na wani bene mai hawa biyu ya rufta a Abuja da safiyar Asabar, inda mutane da dama suka makale a cikin ɓaraguzan ginin.

Ginin da ke kusa da shahararren otal din Cupid da ke kan titin Cupid (Sultan Dasuki Way) a Kubwa a baya wani otal ne mai suna Al-Hilal.

Kara karanta wannan

Mutum 22 sun mutu sakamakon mummunan ibtila'in da ya afka wa ɗalibai a Arewa

Gini ya rufto a Abuja
Mutane sun makale bayan gini ya rufto a Abuja Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Daga baya ya zama asibiti, amma tun da masu asibitin suka bar wurin, ya koma gidan zama, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gini ya rufto a Abuja

Masu bayar da agajin gaggawa da jami'an tsaro suka hallara a wajen da lamarin ya auku.

Sai dai, an samu cikas a ƙoƙarin ceto mutanen saboda har zuwa ƙarfe 8:45 na safe, kayan aikin da ake buƙata domin ceto mutanen ba su iso wajen ba, kusan sa'o'i biyu bayan aukuwar lamarin.

An garzaya da mutane biyu zuwa wani asibiti da ke kusa, yayin da wasu kuma suka tsira da kansu.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa lokacin da ta fito daga gidan bayan ta tashi wajen ƙarfe 7:00 na safe, ta jiyo ƙara wanda hakan ya sanya ta ruga da gudu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban kwaleji, sun bukaci a ba su N70m

Gini ya rufto kan ɗalibai

A wani labarin kuma, kun ji cewa kimanin ɗalibai 200 ne suka makale a ginin makarantar da ya ruguje da safiyar Juma'a, 12 ga watan Yuli, 2024 a jihar Filato.

Kwamishinan yaɗa labarai da sadarwa na jihar Filato, Mista Musa Ashoms ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyara makarantar a Busa Buji da ke yankin Jos.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng