Gwamna Diri Ya Fadi Abin da Zai Faru da Kwamishinoninsa Idan Suka Yi Wasa
- Gwamnan jihar Bayelsa, Duoye Diri, ya yiwa kwamishinoninsa hannunka mai sanda kan tafiyar da al'amuran mulki a jihar mai arziƙin man fetur
- Gwamna Diri ya ba su zaɓi guda biyu na ko su yi abin da ya dace a gwamnati ko kuma ya raba su da muƙaman da ya ɗora su a kai
- Ya bayyana cewa yana da ƙwarin gwiwa kan cewa kwamishionin za su yi abin da ya dace domin sai da aka yi nazari sosai kafin zaɓo su
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bayelsa - Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Duoye Diri, ya ja kunnen kwamishinonin jihar.
Gwamnan ya yi gargaɗin cewa ba zai yi wata-wata ba wajen korar duk kwamishinan da ya kasa taɓuka abin arziƙi ba.
Gwamna Diri ya kuma buƙaci sababbin mambobin majalisar zartarwar jihar da su yi amfani da muradun gwamnatinsa wajen yiwa al'ummar jihar aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane gargaɗi Gwamna Diri ya yi?
Gwamnan ya yi wannan gargaɗin ne a ranar Laraba yayin taron majalisar zartarwar jihar karo na 130 a gidan gwamnatin jihar da ke birnin Yenagoa, babban birnin jihar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Ya bayyana cewa tsare-tsare da shirye-shiryen gwamnatinsa na kawo sauyi sosai ga al'ummar jihar, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
"Kun shigo wannan majalisar zartarwar a daidai lokacin da ake sa ran za mu yi abubuwa da dama. Ku ne idanunmu da kunnuwanmu a waɗannan ma'aikatun."
"Duk wani mamba na majalisar zartarwar wanda bai yi aiki bisa kan tsari da shirye-shiryen da suka yi daidai da wannan gwamnatin ba, za mu raba shi da muƙaminsa.
"Dukkaninku mutane ne masu gaskiya saboda an zaɓo ku ne bayan nazari mai kyau, kuma mun yi amanna cewa za ku yi abin da ya dace."
- Duoye Diri
Gwamnatin Bayelsa ta sauƙaƙawa ma'aikata
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Bayelsa ta ɗauki mataki kan halin kunci da tsadar rayuwa da ake ciki a ƙasar nan.
Gwamnan jihar, Douye Diri ya amince da biyan N35,000 ga ma'aikatan jihar domin rage musu halin ƙunci da wahalar rayuwa da ake ciki.
Asali: Legit.ng