"A Kara Min Lokaci": Tsohon Akanta Janar Zai Dawo da Kudin da Ake Zargin ya Handame

"A Kara Min Lokaci": Tsohon Akanta Janar Zai Dawo da Kudin da Ake Zargin ya Handame

  • Tsohon Akanta janar na kasa Anamekwe Nwabuoku ya nemi kotu ta kara masa lokaci domin biyan Najeriya kudin da hukumar EFCC ta yi zargin ya wawashe
  • Ana zargin Anamekwe Nwabuoku da wawashe Naira Biliyan 1.6bn daga asusun gwamnati tare da karkatar da su da hadin bakin wani mutum guda
  • Gwamnatin Muhammadu Buhari ce ta nada Anamekwe Nwabuoku a matsayin mukaddashin Akanta janar bayan dakatar da Ahmed Idris

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Tsohon Akanta janar na kasa, Anamekwe Nwabuoku ya roki kotu ta kara masa lokaci domin samun damar mayar da kudin da ake zargin ya wawashe.

Hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa (EFCC) ce ke tuhumar Anamekwe Nwabuoku da wani Felix Nweke da kwashe kudin kasar nan da halatta kudin haram da ya kai N1.6bn.

Kara karanta wannan

Aikin Mambila: EFCC za ta gurfanar da Ministan Buhari kan badakalar N33bn

Court
Tsohon Akanta janar ya nemi karin lokaci domin biyan kudin da ake zargin ya kwashe Hoto: Court of Appeal, Nigeria
Asali: Facebook

The Vanguard ta wallafa cewa ana Mista Nwabuoku ya hada baki da daraktan kudi na ma'aikatar tsaro sun wawashe kudin kasa tsakanin shekarar 2019-2021.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nwabuoku ya ce zai mayar da kudin

Gwamnatin Muhammadu Buhari ce ta nada Anamekwe Nwabuoku a matsayin mukaddashin Akanta janar bayan an dakatar da tsohon akanta Ahmed Idris bisa badakalar N80bn.

Jaridar Punch ta wallafa cewa amma an sauke shi makonni bayan nadin a watan Yuli 2022 bisa zargin badakala.

Yayin da aka yi zaman kotu a ranar Laraba, Mista Nwabuoku ya ce a ba shi lokaci zai mayar da sauran kudaden da ke hannunsa.

Lauyansa, Emeka Onyeaka ya shaidawa kotu cewa an samu bullar sabon al'amari a shari'ar, kuma wanda ya ke wakilta zai biya kudin.

Ya kara da cewa tuni Anamekwe Nwabuoku ya mayar da wasu kudin da hukumar EFCC ta gano a wajensa, kuma zai biya sauran nan da wani lokaci.

Kara karanta wannan

Ana fafutukar bawa mata mukaman gwamnati, an gano minista ta kashe miliyoyi kan sayen auduga

Kotu yanke hukunci kan badakalar Emefiele

A wani labarin kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta bayar da umarni ga tsohon gwamnan babban bankin kasa (CBN), Godwin Emefiele.

Kotun ta umarci Mista Emefiele da ya mayar da wasu makudan kudi da ake zargin ya wawashe daga asusun gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.