Assha: Zaune Bata Kare Ba a Najeriya, Wutar Lantarki Ta Sake Baci a Duk Fadin Kasa
- Tushen wutar lantarkin Najeriya ya sake rushewa bayan da aka samu aukuwar hakan a lokuta mabambanta
- Wannan ne karo na hudu da Najeriya ke fuskantar lalacewar wuta tare da jefa ‘yan kasa a duhu a shekarar nan
- A tattaunawar Legit Hausa da wani dan kasuwa a Abuja, ya ce rashin wuta na taba kasuwancinsu ainun
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Najeriya - An sake samun rushewar tushen karafan rarraba wutar lantarki na Najeriya, inda yanzu kasar ke samar da 0.80MW na wutar lantarki.
Binciken da aka yi ya nuna cewa, wutar ta fara raguwa ne da kimanin karfe 2 na rana zuwa 2,797.16MW daga akalla 3,417.99MW da misalign karfe 1 na rana.
Wutar ta kara raguwa zuwa 1,020.08MW da misalin karfe 3 na rana kafin ta karasa raguwa sosai zuwa 0.80MW da misalin karfe 4 na yamma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adadin wutar lantarkin da ake samu a Najeriya yanzu
Daily Trust ta ruwaito cewa, sashen samar da wutar lantarki na Trans-Amadi Power plant ne ya samar da wannan 0.80MW da aka samu.
Wannan shine karo na hudu da turken rarraba wutar lantarkin Najeriya ya rushe a cikin shekarar 2024 da ake ciki yanzu.
Ta tabbata wuta ta lalace a Najeriya
Da yake tabbatar da rushewar, Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Enugu (EEDC) ya ce lamarin ya faru ne kimanin karfe 3:09 na yamma.
Wata sanarwar da aka rabawa manema labarai da shugaban hulda da jama'a na kamfanin, Emeka Ezeh, ya sa wa hannu ta bayyana cewa lamarin ya haifar gimtsewar wutar lantarki a yankunan da hakan ya shafa.
An kara kudin wuta a Najeriya, NLC ta tura bukata
A bangare guda, kungiyar kwadagon Najeriya ta yi kira ga gwamnati da a gaggauta janye karin kudin wutar lantarki da kamfanonin DISCOs suka yi ga abokan huldar na tsarin “Band A”.
Daga ranar 1 ga Yuli, 2024, masu shan wutar lantarki a karkashin tsarin "Band A" za su biya N209.5/KWh maimakon N206.80/KWh da suke biya a baya.
A cikin wata sanarwa da ya aike wa jaridar The Punch, shugaban kungiyar NLC, Kwamared Joe Ajaero, ya bayyana karin a matsayin "tsantsar rashin adalci da girman kai".
Asali: Legit.ng