Sanata Barau Ya Yi Magana Kan Mutuwar Mutum 14 a Masallacin Jumu'a a Kano
- Sanata Barau I Jibirin ya yi jimamin rasuwar Musulmai 14 waɗanda tirela ta murkushe a masallacin Jumu'a a jihar Kano
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa ya yi ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka mutu tare da addu'ar Allah ya tashi kafaɗun waɗanda suka ji raunuka
- Hukumar kiyaye haɗurrra (FRSC) ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:50 na rana a garin Imawa da ke ƙaramar hukumar Kura
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I Jibrin, ya yi ta'aziyyar rasuwar masallata 14 da motar tirela ta bi ta kansu ranar Jumu'a a Kano.
Lagit Hausa ta kawo muku rahoton yadda babbar motar ta muskushe masallatan jim kaɗan bayan sallame Sallar Jumu'a a garin Imawa da ke ƙaramar hukumar Kura.
Hukumar kiyaye haɗurra ta kasa (FRSC) ta tabbatar da mutuwar masallatan sakamakon haɗarin wanda direban tirelar ya gaza shawo kan motar da misalin ƙarfe 13.50 na rana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Barau ya yi ta'aziyya
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Sanata Barau ya nuna damuwa bisa faruwar ibtila'in, inda ya aike da saƙon ta'aziyya ga iyalaan mamatan.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ismail Mudashir ya fitar ranar Asabar, rahoton This Day.
Sanata Barau ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya tashi kafaɗun wadanda suka jikkata cikin kankanin lokaci.
"Cikin yanayin jimami muna alhinin rasuwar masallata 14 waɗanda wata tirela ta murkushe bayan sallar Juma’a a Kano. Muna mika sakon ta'aziyya ga iyalai da abokan arziki.
"Muna addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu ya sa sun huta kuma muna rokon Allah ya sa su a gidan Aljanatul Firdausi."
"Muna rokon Allah maɗaukakin sarki ya bai wa iyalansu haƙuri da juriyar wannan babban rashi."
- Barau Jibrin.
Gini ya danne mutane a Kano
A wani labarin kuma Wani gini da ake kan aiki a Kuntau da ke cikin kwaryar birnin Kano ya rufta kan ma'aikata da wasu mutane ranar Jumu'a.
Rahotanni sun bayyana cewa ginin ya danne mutane 5 ciki hada mai gidan kuma ana fargabar takwas daga ciki sun rasu.
Asali: Legit.ng