ASUU Ta Fara Shirin Shiga Yajin Aiki, Ta Gargadi Gwamnatin Tarayya
- Ƙungiyar malaman jami'a ta Najeriya (ASUU) ta nemi gwamnatin tarayya da ta cika mata buƙatun da take nema a wajenta
- Ƙungiyar ASUU ta yi barazanar cewa za ta shiga yajin aiki nan da makonni biyu idan har ba a cika mata buƙatun ba
- ASUU ta koka kan yadda ba a sauyawa malaman jami'a albashinsu ba a cikin shekara 15 da suka gabata a ƙasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Abia - Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta biya buƙatunta na inganta walwalar malaman jami'a.
ASUU ta yi gargaɗin cewa rashin cika waɗannan buƙatun ka iya sanyawa ta tsunduma cikin yajin aiki nan da makonni biyu.
Shugabar ASUU ta shiyyar Calabar, Misis Happiness Uduk ta bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a jami'ar jihar Abia (ABSU) a ranar Juma'a, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me ASUU ta ce kan shiga yajin aiki?
Ta nuna cewa cika waɗannan buƙatu na da matuƙar muhimmanci domin hana afkawa yajin aikin gama-gari a faɗin ƙasar nan.
Happiness Uduk ta nuna gazawar gwamnatin tarayya wajen cika yarjejeniyar da ta cimmawa da ƙungiyar a shekarar 2009, rahoton jaridar PM News ya tabbatar.
Ta ce hakan ya sanya albashin malaman jami'a bai sauya ba cikin shekara 15 da suka gabata.
"Albashin mambobin ASUU bai sauya ba a cikin shekara 15. Muna kira ga gwamnati da ta kammala tattaunawar da aka fara shekara 13 da suka gabata tare da yin la'akari da halin da tattalin arziƙin ƙasar nan yake ciki a yanzu."
- Misis Happiness Uduk
Ta buƙaci tawagar tattaunawar su gaggauta samar da mafita kan kuɗaɗen ceto jami'o'in gwamnati, biyan kuɗaɗen alawus, albashin da aka riƙe, yawan haraji da muzgunawa mambobin ASUU.
Batun yajin aikin ASUU
A wani labarin kuma, shugaban ƙungiyar malaman jami'o'i (ASUU), Farfesa Emmanuel Osodoke ya ce ƙungiyar na duba yiwuwar janyewa daga kudirin shiga yajin aikin da suka yi niyya a baya.
Farfesa Osodoke ya ce sun fara duba batun ne bayan ganawarsu da jami'an gwamnatin tarayya karkashin jagorancin ministocin Ilimi, Farfesa Tahir Mamman da Dakta Tanko Sununu.
Asali: Legit.ng