Katsina: Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mahaifiyar Fitaccen Mawakin Siyasa Rarara

Katsina: Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mahaifiyar Fitaccen Mawakin Siyasa Rarara

  • Ƴan bindiga sun kai farmaki gidan fitaccen mawakin siyasa, Dauda Adamu Rarara, sun yi awon gaba da mahaifiyarsa a jhar Katsina
  • Legit Hausa ta tattaro cewa maharan sun kutsa sabon gidan Rarara da ke gabashin Kahutu a ƙaramar hukumar Ɗanja jiya da daddare
  • Mazauna garin sun bayyana cewa masu garkuwan sun zo da mugayen makami kuma babu wanda ya iya tunkararsu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kahuta, Katsina - Wasu ƴan bindiga sun shiga garin Kahutu da ke ƙaramar hukumar Ɗanja a jihar Katsina, sun yi garkuwa da mahifiyar Dauda Kahutu Rarara.

Rahotannin da Legit Hausa ta samu da safiyar ranar Jumu'a sun nuna cewa maharan sun ɗauki mahaifiyar fitaccen mawakin siyasar jiya Alhamis da daddare.

Kara karanta wannan

Zamfara: Malamin addinin da ƴan bindiga suka yi garkuwa da shi ya turo saƙo

Dauda Kahutu Rarara da mahaifiyarsa.
Yan bindiga sun yi awon gaba da mahaifiyar Dauda Kahutu Rarara a Katsina Hoto: Dauda Kahutu Rarara
Asali: Facebook

An sace mahaifiyar Rarara a Kahutu

Mazaunan Kahutu sun bayyana cewa ƴan bindigar na ɗauke da manyan bindigu lokacin da suka shiga garin don haka ba a iya tunkararsu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganau sun ce maharan sun kutsa sabon gidan da Rarara ke ginawa a garin Kahutu da karfe 1:00 na dare, suka yi awon gaba da dattijuwar, Hajiya Halima Adamu.

Ana zargin dai ƴan bindigar ba su zo da abin hawa ba, kuma duk da sintirin da ƴan banga ke yi a garin, maharan sun ɗauki dattijowar ba tare da fuskantar turjiya ba.

Yadda aka dauke tsohuwar Rarara a Kahutu

Ɗaya daga cikin masu aikin gini a gidan Rarara ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa suna zargin ƴan bindiga sun bi ta wata babbar taga da ba a kammala aiki ba.

"Ƴan bindigar sun shigo da daddare kuma dama akwai wata taga da ba a gama aikinta ba, ta nan suka bi suka shiga gidan suka ɗauki Hajiya ba tare da ta masu gardama ba."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro, sun sace mutum 20 a Kaduna

Ya ƙara da cewa lamarin ya tayar da hankulan mazauna Kahutu da wasu garuruwan da suke kusa da ita.

Wakilinmu ya tuntuɓi Mubarak Dabai, hadimin Rarara amma ya ce ba a ba su damar magana da manema labarai ba.

Mun samu bayanin cewa jami'an tsaro sun mamaye garin domin fara bincike da kokarin yadda za a ceto matar.

Sai dai har kawo yanzu babu wata sanarwa a hukumanace daga rundunar ƴan sandan jihar Katsina.

Zamfara: Ƴan bindiga sun saki bidiyo

A wani rahoton kun ji cewa Malamin cocin da ƴan bindiga suka yi garkuwa da shi a jihar Zamfara ya turo saƙo mai ɗaga hankali kan halin da yake ciki.

Mikah Suleiman na cocin waliyyi St. Raymond ya roƙi al'umma da gwamnati su taimaka su karɓo shi daga hannun ƴan fashin daji.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel