Ana Fama da Rigimar Sarauta, Gwamna Abba Ya Jiƙa Wa Wasu Yan Kasuwa Aiki a Kano
- Gwamnatin Kano ta umarci ƴan kasuwa su tashi daga wuraren da aka kebe domin shakatawa da hutawa a faɗin jihar
- Kwamishinan mahalli da sauyin yanayi, Nasiru Sule Garo, ya ce mutane sun mayar da wasu lambunan shaƙatawa wurin kasuwanci ba tare da izini ba
- Ya ce a yanzu gwamnati ta shirya gyara irin waɗannan wurare kuma za ta shuka itatuwa domin samar da isasshiyar iskar Oxygen
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta waiwayi wasu wuraren da aka ware domin hutawa da shaƙatawa a jihar.
Ƴan kasuwa sun mamaye irin waɗannan wurare da aka keɓe domin masu hutawa ko shaƙatawa, sun mayar da su wurin hada-hadar kasuwanci.
Gwamnatin Abba ta kora 'yan kasuwan Kano
Sai dai a halin yanzun, Gwamnatin Abba ta umarci dukkan ƴan kasuwar da suka karɓe irin waɗannan wurare su tattara kayansu su tashi, Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na Kano, Nasiru Sule Garo, ne ya ba da wannan umarni ranar Laraba yayin bikin ranar muhalli ta duniya.
Garo ya ce akwai da yawa daga cikin irin wadannan lambuna da wuraren shakatawa na gwamnati a Kano wadanda ‘yan kasuwa suka mamaye.
Me gwamnatin Kano za ta yi a wuraren?
A cewarsa, yanzu gwamnati ta dawo kansu, kuma ta shirya gyara su domin a ci gaba da amfani da su a matsayin lambunan shaƙatawa da hutawa.
Kwamishinan ya ce lambun daura da asibitin Abdullahi Wase da kuma wani da ke kan titin Audu Bako an mayar da su wuraren kasuwanci sabanin dalilin kafa su.
Za a dasa itatuwa miliyan 3 a Kano
Ya ƙara da cewa a wani bangare na aikin dashen itatuwa domin dakile sauyin yanayi, gwamnatin jihar na shirin shuka iri miliyan uku tare da hadin gwiwar ACRSaL da masu ruwa da tsaki.
"An canza mana suna zuwa ma'aikatar muhalli da sauyin yanayi domin tunkarar matsalolin sauyin yanayi na duniya kamar yadda ya shafi Kano."
Garo ya ce baya ga tsaftace magudanar ruwa da matakan daƙile zaizayar kasa, ma’aikatar ta yi feshin magance sauro da kwari a kananan hukumomi 44.
Gobara ta kashe mutum 8 a Kano
A wani rahoton kuma an rasa rayukan mutum takwas kuma kadarorin da suka kai na N31.6m sun salwanta a ibtila'in gobara a jihar Kano a watan Mayu.
Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar, Saminu Yusif Abdullahi ne ya faɗi haka da yake jawabi kan ayyukan hukumar a watan jiya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng