Dattawan Kano Ta Kudu Sun Ɗauki Matsaya Kan Rushe Masarautu 5, Abba Ya Gamu da Cikas

Dattawan Kano Ta Kudu Sun Ɗauki Matsaya Kan Rushe Masarautu 5, Abba Ya Gamu da Cikas

  • Masu ruwa da tsaki a yankin masarautun Gaya, Karaye da Rano sun yi fatali da rushe masarautu biyar da Abba Yusuf ya yi a Kano
  • Sun buƙaci gwamnatin Kano da majalisar dokoki su bi umarnin babbar kotun tarayya wadda ta hana rushe masarautun
  • A makon jiya Gwamna Abba Kabir ya rushe masarautu biyar da Ganduje ya ƙirƙiro kuma ya dawo da Muhammadu Sanusi II

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Masu ruwa da tsaki da dattawa daga yankin masarautun Ƙaraye, Rano da Gaya da aka rushe a kudancin jihar Kano sun juyawa Abba Kabir Yusuf baya.

A yau Laraba, 28 ga watan Mayu, 2028, masu ruwa da tsakin suka buƙaci Gwamna Abba ya gaggauta mayar da sarakunan da ya sauke.

Kara karanta wannan

Wa zai zama Sarkin Kano? Abin da kotuna 2 suka ce game da makomar Sanusi II da Aminu

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Masu ruwa da tsaki a Kano ta Kudu sun nemi Gwamna Abba ya dawo da sarakunan Gaya, Rano da Ƙaraye Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

The Nation ta tattaro cewa masu ruwa da tsaki da dattawa 103 ne suka cimma wannan matsaya kuma sun kunshi mutanen dukkan kananan hukumomin Kano ta Kudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dattawa sun bukaci a dawo da Sarakuna

Dattawan na shiyyar Kano ta Kudu un yi kira ga gwamnatin Kano da majalisar dokoki su yi biyayya ga umarnin babbar kotun tarayya na dawo da sarakunan da aka rusa.

Daga cikin manyan mutanen da suka rattaba hannu kan wannan matsaya har da ɗan majalisar tarayya, Honorabul Ado Doguwa.

Sauran sun haɗa da Sanata Mas’ud El-Jibrin, Hon. Musa Salihu, Dr. Ali Musa Burun-Burun, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, Farfesa Shehu Musa, Farfesa Andu Salihu Kabiya da Manjo Janar AT Jibrin da sauransu.

"Illar sauke sarakunan Kano"

Mai magana da yawunsu, Musa Salihu Doguwa wanda tsohon kwamishina ne ya ce tsige sarakunan wata barazana ce ga dinbin ci gaban da tsohuwar gwamnati ta kawo.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da ruɗanin hukuncin kotuna 2, jigon NNPP ya yi magana kan naɗin Sarkin Kano

Doguwa ya ƙara da cewa sauke sarakunan ba tare da wani dalili ko bin ƙa'ida ba, zalunci ne da ya zama wajibi a dawo a gyara.

A rahoton jaridar Vanguard, tsohon kwamishinan ya ce:

"Matakin da majalisar dokoki ta ɗauka na gyara dokar masarautu da kuma amincewa nan take da gwamna ya yi wani gagarumin koma baya ne ga ci gaban waɗannan masarautu.
"Muna kira ga gwamnatin Kano da majalisar dokokin su bi doka tare da bin umarnin babbar kotun tarayya ta hanyar gaggauta dawo da masarautun domin gudun barkewar rikicin."

Ƴan majalisar APC sun gana da Sarki

A wani rahoton kuma mambobi 12 na majalisar dokokin jihar Kano sun yi mubaya'a ga sarki na 15, Aminu Ado Bayero a ƙaramar fadar Nasarawa.

Ƴan majalisar na jam'iyyar APC mai hamayya a Kano sun ziyarci basaraken a fadar da yake zaune ranar Talata, 28 ga watan Mayu, 2024.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta umarci a fitar da Muhammadu Sanusi II Daga Fadar Sarki

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel