Aminu Ado: Dalilin Kotu na Umartar Jami'an Tsaro Su Fitar da Sarkin Kano na 15 daga Fada
- Babbar kotun jiha ta bayar da umarni guda uku kan sarkin Kano na 15 da sauran sarakuna huɗu da Abdullahi Ganduje ya naɗa
- A wata hira da mai magana da yawun kotunnan jihar, ya bayyana abin da ya sa kotun ta ɗauki wannan mataki a ƙarar da aka shigar
- Jami'in ce kotun ta sanya ranar da za a dawo domin sauraren hujjojjn kowane ɓangare gabanin ta yanke hukuncin karshe
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Babbar kotun jihar Kano ta umurci rundunar ƴan sanda da sauran jami'an tsaro su fitar da sarki na 15, Aminu Ado Bayero daga karamar fada da ke Nassarawa.
Kotun ta ɗauki wannan matakin ne a ƙarar da aka shigar gabanta kan taƙaddamar sarautar da ke faruwa a jihar tun bayan dawo da Sarki Muhammadu Sanusi.
Sarkin Kano: Meyasa kotu ta ɗauki mataki?
A wata hira da DCL Hausa, mai nagana da yawun kotunan jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim ya ce kotu ta umarci jami'an tsaro su fitar da sarkin daga fadar cikin gaggawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ta kuma umarci dukkan sarakuna biyar da aka tsige su daina bayyana kansu a matsayin sarakuna har sai ta yanke hukuncin karshe a ƙarar.
Ibrahim ya ce kwamishinan shari'a na Kano, kakakin majalisar dokoki da ita kanta majalisar dokokin ne suka shigar da wannan ƙara.
Umarnin kotu kan sarakunan Kano
Da yake jawabi kan umarnin kotu, Baba Jibo Ibrahim.ya ce:
"Bayan gabatarwa daga lauyan masu ƙara, kotu ta ba da umarni guda uku. Na farko an kange waɗannan sarakuna biyar daga bayyana kansu a matsayin sarakuna.
"Sannan ta umarci kwamishinan ƴan sanda ya fitar da mai martaba sarki na 15 daga gidan sarauta da ke titin gidan gwamnati har zuwa lokacin da aka saurari gundarin karar.
"A ƙarshe kotun ta bayar da umarnin kwamishinan ƴan sanda ya sadar da kwafin takardar wannan hukunci ga sarakuna daga na ɗaya har zuwa na biyar domin a tabbatar da bin doka da oda."
Za a yi shari'a kan masarautun Kano
Kakakin kotun ya kuma yi bayanin cewa dukkan waɗannan umarni na wucin gadi ne, za a dawo a baje kolin hujjoji tsakanin kowane ɓangare kafin kotu ta yanke hukunci.
A karshe, ya ce kotun ta ɗage zaman zuwa watan Yuni domin a dawo a saurari gundarin korafin da masu kara suka shigar.
Aminu Ado Bayero yana zaune ne a ƙaramar fadar sarki da ke kan titin gidan gwamnati a cikin birnin Kano tun ranar Asabar.
Sarki Sanusi ya gana da jami'an tsaro
A wani rahoton kuma, an ji wata majiya ta bayyana kalaman da Sarki Muhammadu Sanusi II ya faɗawa manyan jami'an tsaro a ganawar da suka yi a Kano.
Sarkin ya faɗawa shugabannin tsaro cewa umarnin kotu na hana mayar da da shi kan sarauta hayaniyar soshiyal midiya ce.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng