Abubuwa Sun Caɓe, Jami'an Tsaro Sun Mamaye Gidan Gwamnatin Jihar Kano

Abubuwa Sun Caɓe, Jami'an Tsaro Sun Mamaye Gidan Gwamnatin Jihar Kano

  • Jami'an tsaro cikin shirin ko ta kwana sun mamaye muhimman wurare a gidan gwamnatin jihar Kano yau Asabar, 25 ga watan Mayu
  • Wannan mataki na ƙara tsaurara tsaro na zuwa ne a lokacin da taƙaddama kan kujerar Sarkin Kano ke ƙara dagulewa
  • Rahotanni sun bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na fadar sarki da ke Kofar Kudu tun lokacin da ƴa raka Muhammadu Sanusi II

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka an tsaurara matakan tsaro a gidan gwamnati Kano a lokacin da taƙaddama kan sarauta ke ƙara rincaɓewa.

Jami'an tsaro sun mamaye muhimman wurare a gidan gwamnatin duk da ba su hana shige da fice a gidan gwamnatin ba.

Kara karanta wannan

Manyan jami'an tsaro sun yi watsi da Gwamna, sun isa ƙaramar fadar sarkin Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
An tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen fadar gwamnatin Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Wakilin jaridar Daily Trust ya lura da cewa babban jami’in tsaro na Gwamna Abba Kabir Yusuf na cikin damuwa matuƙa, fuskarsa ta nuna hakan a lokacin da yake tafiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai har kawo yanzun bai yarda ya ce komai game da abubuwan da ke faruwa ba musamman ganin an kara girke jami'an tsaro a gidan gwamnati.

A ɗazu dai shugabannin hukumomon tsaro na jihar suka gana da Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero a ƙaramar fadar Ƙofar Kudd..

Sai yanzu haka rahotanni sun nuna cewa manyan jami'an tsaro na cikin gidan gwamnatin Kano suna wani taron na daban.

Gwamna na fadar Sarki

Har yanzu dai Gwamna Abba Kabir Yusuf na can fadar Sarki tun lokacin da ya raka Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II da safiyar yau.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya ɗauki zafi, ya ba da umarnin a kama tsohon Sarkin Kano

An tattaro cewa an ga ayarin motocin gwamnan a fadar sarki sa'o'i kaɗan da suka wuce, ma'ana dai har yanzun yana can.

Tun da safe dai Gwamna Abba ya umarci yan sanda sun tsare Aminu Ado Bayero, amma jami'an tsaron sun ce ba zasu kama shi ba, cewar rahoton The Nation.

Shugabannin tsaro sun gana da Aminu Ado

A wani rahoton kuma Shugabannin tsaro a jihar Kano sun isa ƙaramar fadar Sarki ta Ƙofar Kudd, inda tsohon sarki Aminu Ado Bayero ke ciki

Wannan na zuwa ne mintoci kaɗan bayan hukumomin tsaron jihar sun ce ba za su bi umarnin Gwamna Abba na kama tsohon sarkin Abba

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel