Yadda Aka Hana Aminu Ado Bayero Shiga Kano Bayan Sauke Shi Daga Sarauta

Yadda Aka Hana Aminu Ado Bayero Shiga Kano Bayan Sauke Shi Daga Sarauta

  • Gwamnatin jihar Kano ta hana mai martaba sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero shiga jihar a yammacin jiya Alhamis
  • Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin ta kara da kwace rukunin mototin da sarkin ke amfani da su domin gudanar da ayyukan fada
  • Ana tunanin cewa sarki Aminu Bayero ya yi yunkurin shiga Kano ne domin tattara kayansa kamar yadda aka ba su wa'adin sa'o'i 48

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

A jiya Alhamis ne sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi yunkurin shiga Kano bayan an sanar da sauke shi daga sarautar jihar.

Aminu Ado
Gwamnati ta hana Aminu Ado Bayero shiga Kano. Hoto: @KabiruMisali
Asali: Twitter

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa gwamnatin jihar karkashin Abba Kabir Yusuf ta hana sarkin shigowa garin saboda wasu dalilai.

Kara karanta wannan

Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano daga mayar da Sanusi II gidan sarauta

Yadda aka hana Aminu Bayero shiga Kano

Bayan Abba Kabir Yusuf ya ba sarakunan da ya sauke sa'o'i 48 su fice daga fada, Aminu Ado Bayero ya nufi Kano daga jihar Ogun domin tattara kayansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma sai dai gwamnatin jihar ta ba jami'an tsaro umurnin hana shi shigowa garin domin kaucewa barkewar rikici.

Har ila yau gwamnatin jihar ta bada umarnin kwace dukkan motocin fada da Aminu Ado Bayero ke amfani da su.

Kamar yadda gwamnatin jihar ta bada umurni, a yanzu haka an tattara motocin a fadar masarautar jihar Kano ana sauraron isowar Muhammadu Sanusi II.

Sarakunan da aka sauke a Kano

Rusa dokar masarautu da gwamnatin jihar Kano ta yi a jiya Alhamis ta shafi manyan sarakuna guda biyar.

Sarakunan sun hada da sarkin Kano, Gaya, Rano, Karaye da Bichi amma sai dai lamarin sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya fi daukar hankali.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa Gwamna Abba ya mayar da Sanusi II kan kujerar Sarkin Kano

Bashir Ahmad ya caccaki majalisar Kano

A wani rahoton, kun ji cewa kudirin da majalisar Kano ta tabbatar ya cigaba da tayar da kura daga cikin da wajen jihar ta yadda al'umma ke bayyana ra'ayoyi mabanbanta.

Hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya tofa albarkacin bakinsa kan rusa masarautun Kano da majalisar ta yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel