Rikicin Shugabancin Daba: Mutum 3 Sun Mutu Yayin da Wani Faɗa Ya Ɓarke a Kano
- An rasa rayuka yayin da faɗa ya ɓarke tsakanin kungiyoyin ƴan daba a yankin ƙaramar hukumar Tarauni a jihar Kano
- Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ƴan sanda sun kai ɗauki kuma sun tarwatsa ƴan daban
- Lamarin dai ya auku ne a wurin wani bikin al'ada na mafarauta da aka shirya domin murnar aure ranar Lahadi da yamma
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Mutum uku sun rasa rayuwarsu yayin da aka yi arangama tsakanin ƙungiyoyin ƴan daba masu adawa da juna a Darmanawa, ƙaramar hukumar Tarauni a jihar Kano.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta kawo labarin, lamarin ya faru ne kan taƙaddamar shugabanci tsakanin ƴan daban ranar Lahadi da yamma.
Yadda ƴan daban suka gwabza da juna
Rikicin ya fara ne bayan wani Muhammad Barde, mai shekara 59, ya shirya taron Gangi (wani bikin al'ada na mafarauta) domin murnar auren ƴaƴansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai abin takaicin ɓata garin sun yi amfani da wannan dama suka farmaki junansu kan lamarin shugabanci.
Da yawa daga cikin ƴan daban sun fitar da makamai nan take kuma cikin ƙanƙanin lokaci faɗa ya ɓarke a wurin.
Wane mataki ƴan sandan Kano suka ɗauka?
Da yake ƙarin bayani kan lamarin, mai magana da yawun rundunar ƴan sanda na jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ƴan sanda sun kai ɗauki bayan samun rahoto.
Ya ce bayan samun kiran gaggawa, ƴan sanda sun garzaya wurin kuma suka tarwtasa dukkan ƴan daban, cewar rahoton Nigeria News.
Sai dai 'yan sa'o'i kadan bayan haka ƴan daban suka ci gaba gwabza fada tsakanin su, lamarin da ya kai ga 'yan sanda suka sake shiga tsakani.
Kiyawa ya ce rikicin ya yi sanadin mutuwar, Sadiq Abdulkadir mai shekaru 23 ɗan yankin Darmanawa da Muhammad Sani mai shekaru 22 ɗan unguwar Sallari.
Kakakin ƴan sandan ya ce kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, Usaini Gumel ya bayar da umarnin kama wanda ya shirya taron tare da wasu mutane biyu nan take.
Kano: An harbe matashin da ba ruwansa
Wani matashi, Sadiq Abdullahi mai shekaru 18 a unguwar Karkasara, ya mutu sakamakon harbin da ya same shi a lokacin da ‘yan sanda ke kokarin tarwatsa ‘yan barandan.
Mahaifin yaron, Malam Abdullahi Ya-Sayyadi, ya ce yana makaranta aka kira shi daga asibitin koyarwa na Aminu Kano domin ya tabbatar da ko ɗansa ne ya mutu bayan harsashi ya same shi a ciki.
Rundunar ‘yan sandan ta ce za a gudanar da cikakken bincike tare da sanar da duka abinda aka gano yayin da Malam Ya-Sayyadi ya ce ya bar wa Allah komai.
Ƴan sanda sun kama ƴan canji
A wani rahoton kuma ƴan sanda da haɗin guiwar jami'an DSS sun damƙe ƴan canjin da suka yi haye a kasuwar musayar kuɗi Wapa da ke jihar Kano.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Usaini Gumel ya ce jami'an sun kama waɗanda ake zargi 29 amma daga bisani aka wanke 12 daga cikinsu.
Muhammad Malumfashi, babban editan sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng