Hukumar EFCC Ta Kama Manyan Jami'an Tsaro 6 Kan Badaƙalar N6bn
- EFCC ta fara gudanar da bincike kan badaƙalar wasu maƙudan kuɗi har N6bn a hukumar tsaro na farar hula (NSCDC)
- Rshotanni sun nuna cewa jami'an hukumar EFCC sun tsitsiye manyan jami'an NSCDC shida yanzu haka a hedkwatarsu da ke Abuja
- Tun farko shugaban EFCC na ƙasa ne ya buƙaci a miƙa masa jami'an kuma babban kwamandan sibil difens ya ba da umarnin a kama su
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta kama wasu manyan jami’an hukumar tsaron sibil difens (NSCDC) guda shida.
Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka manyan jami'an tsaron na hannun jami'an EFCC suna amsa tambayoyi a hedkwatar hukumar da ke Jabi a birnin Abuja.
Ana zargin NSCDC a badakalar N6bn
Jami'an hukumar EFCC sun titsiye su bisa zargin hannu a badaƙalar wasu maƙudan kuɗaɗe da suka kai N6bn.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da babu cikakkun bayanai kan wannan bincike amma jaridar Punch ta tattaro cewa an miƙa jami'an NSCDC ga EFCC ranar Litinin bisa umarnin babban kwamanda, Ahmed Audi.
Wasu majiyoyi masu tushe sun ce tun farko shugaban EFCC na ƙasa, Ola Olukoyede, ya tura takarda zuwa ga shugaban NSCDC, inda ya buƙaci ya miƙa jami'an domin bincike.
Wata majiya ta ce:
"Yanzu haka manyan jami'an hukumar NSCDC shida na tsare a hannun mu. Masu bincike sun titsiye su da tambayoyi kan zargin almundahanar da ta kai ta N6bn."
EFCC ta kama kwamandan NSCDC?
Haka nan kuma wata majiyar ta daban ta bayyana cewa EFCC ba ta cafke shugaban rundunar NSCDC ba kuma ba ya cikin waɗanda ake bincike a kansu.
"EFCC ba ta kama babban kwamandan NSCDC na ƙasa ba, kuma ba a bincike a kansa, kawai dai mun tsare wasu jami'ai manya guda 6 kuma ana bincike a kansu kan satar N6bn."
Hukumar EFCC ba tayi magana ba
Ba a samu jin ta bakin kakakin EFCC na ƙasa, Dele Oyewale, kan wannan lamarin ba domin bai ɗaga kiran waya ko amsa sakonnin tes da aka tura masa ba.
Amma yayin da aka tuntube shi, mai magana da yawun NSCDC, Babawale Afolabi, ya ce bai da masaniya kan wannan bincike, rahoton Business Day.
SERAP ta kama gwamnoni a kotu
A wani rahoton kuma, SERAP ta maka gwamnonin Najeriya a kotu kan yadda suke cin bashin manyan kudade ba tare da yiwa ‘yan kasa bayani ba.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ake ci gaba da taso ‘yan siyasar kasar nan a gaba kan yadda suke cin bashi ba tare da tunanin yadda za a biya ba.
Asali: Legit.ng