Badaƙalar N8bn: EFCC Za Ta Gurfanar da Tsohon Ministan Buhari a Gaban Kotu
- EFCC ta shirya za ta gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika a gaban kotu a mako mai zuwa
- Hukumar ta kama Sirika ne bisa tuhumar da ta shafi wasu kwangiloli da ya bayar na sama da N8bn ga ɗan uwansa, Abubakar Sirika
- A makon da ya gabata ne jami'an EFCC suka tsare Sirika na tsawon sa'o'i kuma ta kama ɗan uwan nasa daga baya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC), ta shirya tsaf za ta gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika a gaban kotu.
EFCC za ta gurfanar da tsohon ministan, wanda ya yi aiki a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a gaban kotu a cikin makon gobe.
An kama tsohon ministan ne a farkon makon nan kan zargin zamba da bada kwangila ga dan uwansa, Abubakar, wani ma’aikacin gwamnati, har ta Naira biliyan 8.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abubakar Sirika mataimakin darakta ne a ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya, kamar yadda jaridar Leadership ta tattaro.
Binciken da EFCC ta gudanar ya nuna cewa Sirika ya bai wa dan uwansa kwangiloli duk da ya san cewa ma’aikacin gwamnati ne.
Tuhume-tuhumen da ake wa Sirika?
Majiyoyin EFCC sun ce Sirika zai fuskanci tuhuma kan binciken da ake yi da ya shafi zamba da karkatar da kudade sama da Naira biliyan 8.
Wasu daga cikin tuhume-tuhume sun shafi badaƙalar kwangilar filin jirgin sama na Katsina, sanya na'urori a filin jirgin Abuja, sayen jirgin Magnus da kwalejin koyon tuƙin jirgi ta Zariya.
Kwangila ta farko da ake da binciken tsohon ministan a kanta ita ce ya bai wa kamfanin Engirios Nigeria Limited domin gina tasha a filin jirgin Katsina kan kuɗi N1,345,586,500.
Ta biyu kuma Sirika ya ba da ita a ranar 3 ga Nuwamba, 2022 don kafa wata cibiyar kula da manyan motoci ta kashe gobara a filin jirgin sama na Katsina kan Naira biliyan 3.8 da sauransu.
Jami'an EFCC sun tsare Hadi Sirika na tsawon sa'o'i a ofishinsu na Abuja yayin da hukumar ta kama ɗan uwansa Abubakar Sirika, This Day ta ruwaito.
Tinubu ya naɗa shugabanni 2
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shugabannin da za su jagoranci wasu hukumomin gwamnatin tarayya guda biyu ranar Jumu'a.
Shugaban ya naɗa Dokta Innocent Bariate Barikor a matsayin shugaban hukumar NESREA da Prince Ebitimi Amgbare a matsayin shugaban NDRBDA.
Asali: Legit.ng