EFCC Ta Tsare Ministan Buhari Bisa Zargin Almundahanar Biliyoyin Kudi

EFCC Ta Tsare Ministan Buhari Bisa Zargin Almundahanar Biliyoyin Kudi

  • Hukumar EFCC mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta kama tsohon ministan Muhammadu Buhari, Hadi Sirika.
  • EFCC ta kama shi ne bisa zargin sa da hannu cikin badakallar kudi sama da naira biliyan takwas a lokacin da yake minista
  • Hadi Sirika dai yana daga cikin ministotin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da ake zargi da cin hanci da rashawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum

Abuja - Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta kama tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika.

Hukumar na zarginsa ne da hannu cikin bincike da ta ke a kan almundahanar kudi da ya haura Naira biliyan takwas.

Kara karanta wannan

Katsina: Yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC, sun kashe jami'in tsaro

EFCC ta kama Hadi Sirika bisa zargin sace bilyan 8. Hoto: FAAN/EFCC
EFCC Ta Kama Hadi Sirika Bisa Zargin Al’mundahanar Biliyan 8
Asali: Facebook

Yaushe EFCC ta kama Hadi Sirika?

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Hadi Sirika ya isa ofishin EFCC da ke Abuja ne yau Talata da misalin karfe 1.00 na rana domin gudanar da bincike.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tabbatar da cewa ana bincikensa ne a kan wata kwangila da ya ba kamfanin dan uwansa mai suna Engirious Nigeria Limited wanda mallakin kaninsa ne.

Jami'a hukumar da ba sa so a bayyana sunan su sun tabbatar da cewa hukumar ta kama tsohon ministan a yau watau Talata.

EFCC: Dalilin rike Sanata Hadi Sirika

Jami'an sun tabbatar da cewa an kama shi ne bisa zarginsa da hada kai da dan uwansa wurin karkatar da makudan kudade sama da biliyan 8, a cewar jaridar Leadership

Tun a watan Fabrairu dai aka ruwaito cewa hukumar ta EFCC ta fara binciken ofishinsa bisa baba-kere da dukiyar al'umma.

Kara karanta wannan

FCTA: Wike ya kaddamar da rusa gidajen mutane a Abuja, bayanan rusau sun fito

Hadi Sirika yana cikin ministotin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da hukumar EFCC ke nuna wa yatsa bisa zargin karkatar da kudade.

EFCC ta kama 'danuwan Hadi Sirika

A wani rahoton kuma, kun ji cewa Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta cafke Abubakar Ahmad Sirika, kanin tsohon ministan sufurin jiragen sama

An tattaro cewa, hukumar ta bugi ruwan cikinsa a binciken da ta ke yi na yadda aka karkakatar da biliyoyin kudade daga ma'aikatar sufurin jiragen sama

Ana zargin an bai wa Ahmad Sirika, kwangila na biliyan 8 ta kamfaninsa mai suna Engirios Nigeria Limited

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng