SSANU da NASU Sun Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki a Jami'o'in Najeriya, Sun Faɗi Dalili

SSANU da NASU Sun Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki a Jami'o'in Najeriya, Sun Faɗi Dalili

  • Mambonin kungiyoyin SSANU da NASU sun yi barazanar shiga yajin aiki idan har gwamnatin tarayya ta ki biyansu albashinsu da ta rike
  • Mambobin kungiyar ta ma’aikatan jami’o’i marasa koyarwa, ta ce gwamnatin tarayya ta biya 'yan ASUU albashinsu amma ta ki biyan nasu
  • Kungiyoyin sun ce gwamnati ba ta yi komai ba bayan sun rubuta wata wasika zuwa ga Shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, da ministan ilimi, Tahir Mamman

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

FCT, Abuja - Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU) da takwararta ta Ma’aikatan Jami’o’i Marasa Koyarwa (NASU), sun ba gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki bakwai ta saki albashin mambobinsu.

Kwamitin hadin gwiwa na kungiyoyin sun ce za su shiga yajin aiki idan har ba a saki albashinsu da gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta rike ba a yayin yajin aikinsu a 2022.

Kara karanta wannan

Yadda aka damke shugabannin kamfanin Binance daga kasar waje a yunkurin karya Dala

Ma'aikatan jami'o'i da nasa koyarwa suna shirin shiga yajin aiki
SSANU da NASU Sun Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki a Jami'o'in Najeriya, Sun Faɗi Dalili Hoto: @SSANU_NATIONAL
Asali: Twitter

Me yasa kungiyoyin ke barazanar tsunduma yajin aiki?

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, hakan na kunshe ne a cikin wata wasikar hadin gwiwa da shugaban SSANU, Muhammed Ibrahim da babban sakataren NASU, Peters Adeyemi, suka sanyawa hannu a ranar Juma'a, 1 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyoyin sun ce gwamnatin tarayya ta saki albashin 'yan ASUU na watanni hudu amma ta ki sakin albashin ma'aikatan da basa koyarwa da ta rike.

SSANU da NASU sun aika takarda ofishin Gbajabiamila

An tattaro cewa kungiyoyin sun rubuta wasikun zanga-zanga kan haka zuwa ga Shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, da minsitan ilimi, Tahir Mamman, a ranar 13 ga watan Fabarairun 2024.

Wasikar da kungiyar SSANU ta wallafa a shafinta na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) @SSANU_NATIONAL, na cewa:

“Saboda haka, muna sake amfani da wannan damarwajen yin kira ga Gwamnatin Tarayya da ta yi abin da ya kamata cikin kwanaki bakwai masu zuwa.

Kara karanta wannan

Naira Miliyan 1 muke so a matsayin mafi karancin albashi a wata Inji Kungiyar NLC

"Kada a ga laifin kwamitin hadin gwiwa na NASU da SSANU idan aka tsayar da harkoki cak a jami'a, saboda mun yi hakuri sosai.
"Idan gwamnatin tarayya bata yi komai don magance lamarin nan ba sannan ta ki amsa wasikun baya da muka tura masu, za a tilastawa mambobin kungiyoyin biyu daukar matakan da suka dace kan lamarin."

Gwamnati ta fara biyan 'yan ASUU

A gefe guda, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa gwamnatin tarayya ta fara biyan albashin malaman jami’o’i a ƙarƙashin ƙungiyar malaman jami’o’i ta ASUU da aka riƙe.

'A gefe guda, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa gwamnatin tarayya ta fara biyan albashin malaman jami’o’i a ƙarƙashin ƙungiyar malaman jami’o’i ta ASUU da aka riƙe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng