An Kama Fasto Ɗan Shekara 65 Kan Haikewa Ƴar Shekara 9 a Ogun

An Kama Fasto Ɗan Shekara 65 Kan Haikewa Ƴar Shekara 9 a Ogun

  • Wani malamin coci, Timothy Adedibu ya shi hannu bisa zargin haike ma yarinya yar shekara 9 a Jihar Ogun
  • Jami'an yan sanda sun kama Faston mai shekaru 65 bayan kawun yarinyar ya shigar da korafi
  • Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar, Omolola Odutola ya ce za a mayar da lamarin hedikwatar yan sandan jihar don fadada bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Magboro, Jihar Ogun - Wani Malamin coci mai shekaru 65 mai suna Timothy Adedibu ya shiga komar yan sanda bisa zargin haikewa yarinya mai shekaru 9 a Magboro, karamar hukumar Obafemi Owade da ke Jihar Ogun.

Kamar yadda Punch ta ruwaito, wanda ake zargin, limamin wata coci da ke yankin ya shiga hannu bayan kawun yarinyar ya shigar da korafi ranar Alhamis, 15 ga Fabrairu.

An kama babban fasto kan haikewa yar shekara 9 a Ogun
'Yan sanda sun kama Fasto Adedibu kan haikewa 'yar shekara 9 a Ogun. Hoto: Rundunar 'Yan Sanda
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Zaki ya kashe mai bashi abinci da ya shafe shekaru 9 yana rainonsa a jami'ar Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda malamin coci ya haikewa yarinya

A cewar iyalan yarinyar, Fasto Adedibu ya yaudari yarinyar zuwa gidansa kuma ya yi lalata da ita.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, Omolola Odutola, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce suna cigaba da bincike.

"An kama Faston. An bawa iyalan dama da su kai yarinyar asibiti ayi mata gwaje-gwaje da magani.
Za a mayar da lamarin zuwa hedikwatar yan sanda don fadada bincike."

Faston ka iya shan daurin rai da rai

Da yake sharhi kan lamarin, wani masanin shari'a da kare hakkin dan adam, Collins Aigbogun, ya ce duk wanda aka kama da irin laifin zai kare rayuwarsa a gidan gyaran hali.

"Lalata kananan yara ba maganar kundin dokar kasa ba ne, magane ce ta cin zarafin dan Adam.
"Haikewa yarinya yar kasa da shekara 13, duk wanda aka tabbatar ya yi laifin za a yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Jihar Ogun da Lagos duk dokar daya ce."

Kara karanta wannan

Yadda wani mutum ya hallaka makwabcinsa saboda akuya, ya shiga hannun ‘yan sanda

“Ina Son Mahaifinsa Idan Yana Raye Don Allah”: Matashiya Ta Fadi Dalilinta Na Auren Dattijo

A wani rahoton, bidiyon wata matashiya yar Najeriya wacce ta bayyana dalilinta na auren tsoho ya ja hankalin jama'a a TikTok.

Matashiyar ta tuna cewa tana aiki ne a matsayin mai karbar baki lokacin da ta hadu da dattijon wanda ya sauya rayuwarta.

Mutumin ya sanya ta makarantar koyon girke-girke, ya sama mata shago, sannan ya fara kula da ita har zuwa lokacin da ya nemi aurenta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164