Akwai Matsala Yayin da Majalisar Dokoki Ta Juya Wa Gwamnan PDP Baya, Ta Amince da Abu 4

Akwai Matsala Yayin da Majalisar Dokoki Ta Juya Wa Gwamnan PDP Baya, Ta Amince da Abu 4

  • Majalisar dokokin jihar Ribas ta aiwatar da sabbin kudurori guda hudu bayan ta kada kuri'ar yin watsi da Gwamna Siminalayi Fubara
  • Kakakin majalisar, Martin Amaewhule ya bayyana cewa Fubara ya ki amincewa da kudurorin a wasu wasiku mabanbanta guda hudu
  • Amaewhule ya bayyana cewa a karkashin sashe na 100 ba a bukatar gwamna ya amince da kudirorin kafin su zama doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Port Harcourt, jihar Rivers - Majalisar dokokin jihar Ribas ta aiwatar da wasu kudurori hudu sun zama doka ba tare da amincewar Gwamna Siminalayi Fubara ba.

Yan majalisar sun yanke shawarar ne bayan kada kuri'ar yin watsi da gwamnan a yayin zaman majalisar a ranar Juma'a, 26 ga watan Janairu, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

A karo na biyu, gwamnan PDP ya rantsar da sabbin kwamishinoni 9 bayan sun yi murabus

Majalisar Ribas ta yi watsi da gwamna wajen aiwatar da wasu dokoki
Akwai Matsala Yayin da Majalisar Dokoki Ta Juya Wa Gwamnan PDP Baya, Ta Amince da Abu 4 Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Sabbin kudurorin da yan majalisar suka sa hannu don zama doka kamar yadda aka sabunta sune:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

  • Dokar kananan hukumomin Ribas
  • Dokar sarakunan gargajiya ta jihar Ribas
  • dokar talla da haramcin amfani da kayayyaki mallakin jihar Ribas
  • Dokar kula da kudade da ba fannin kudin jihar Ribas 'yancin gashin kai

Kakakin majalisar, Martin Amaewhule ya karanto wasikai hudu inda Gwamna Fubara ya ki amincewa da sabbin dokokin da aka tura masa don ya yarda da su.

Amaewhule ya yi bayanin cewa majalisar ta dogara da sashi 100 karamin sashi na 5 wanda ya ce ba a bukatar amincewar gwamna don aiwatar da kudirorin su zama doka.

A cewar jaridar Leadership, kakakin majalisar ya yi zargin cewa Gwamna Fubara ba shi da niyar gudanar da zabukan kananan hukumomi a jihar.

“Babban abu a nan shi ne wannan doka ta cire ikon Gwamna na nada shugabannin kwamitocin riko na kananan hukumomi, Gwamna bai ji dadin yadda muka cire ikon da yake da shi na nada shugabannin riko ba.”

Kara karanta wannan

Rundunar Soji ta tona asirin mutum 2 da ƙarin wasu abubuwa da suka jawo kashe-kashe a Filato

Gwamna Fubara ya rantsar da kwamishinoni

A wani labarin kuma, Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya rantsar da kwamishinoni tara da ya sake naɗawa a karo na biyu bayan sun yi murabus.

Bikin ranstuwar kama aikin kwamishinonin ya gudana ne a ɗakin taron majalisar zartarwa da ke gidan gwamnati a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng