"A Nemo Mun Ita: Bidiyon Wata Yar Makaranta Tana Sallah a Kan Hanya Ya Dauka Hankalin Jama'a
- Jama'a sun yi cece-kuce kan bidiyon wata yarinyar musulma sanye da kayan makaranta tana sallah a titi
- Yarinyar ta yi amfani da jakarta wajen kare gabanta saboda masu wucewa, inda tayi sujjada a kansa yayin da take bin jam'in sallar da ke tashi a lasifika
- Yayin da jajircewarta kan addininta ya taba zukata da dama, wasu sun nuna damuwa dangane da abun da ta aikata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
A cikin wani bidiyo da yadu, an gano wata yarinya musulma tana sallah sanye da kayan makaranta a titi.
Yarinyar wacce alamu suka nuna tana a hanyarta ta dawowa daga makaranta ne ta tsuma zukata da jajircewarta kan addini.
A cikin bidiyon, yarinyar ta yi amfani da jakar makaranta don kare gabanta daga masu tafiya, kuma bata damu da mutanen da ke wucewa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta yi sujjada kan jakar yayin da take bin jam'in sallar da ke tashi daga wani masallaci
Shafin @sarhmymoore ne ya wallafa bidiyon a TikTok kuma an samu mutane fiye da 186k da suka kalla a daidai lokacin kawo rahoton nan.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
konibaje3 ya ce:
"Na rantse sai da hawaye ya zuba daga idanuna. Me zai haka ka karbar Allah? Allah Ya albarkace ta."
Haykay_Global ya ce:
"Don Allah ku nemo mun wannan yarinyar zan bata 50k."
nafiudanladi480 ya ce:
" Allah madaukakin sarki ya amsa ibadunmu ya ku yan uwana, don Allah kada ku ga laifinta..."
Senior Man ya ce:
"Duk da cewar ni Kirista ne, na sani a cikin raina Allah ya karbi addu'arki yar'uwata, abun alkhairi ne ka daraja mahaliccinka."
Babban fasto zai gina katafaren masallaci
A wani labari na daban, Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Ayodele, ya sanar da aniyarsa na gina katafaren masallaci na miliyoyin naira a jihar Legas.
Mai ba shi shawara kan harkokin labarai, Osho Oluwatosin ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya gabatarwa manema labarai, a ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu, Nigerian Tribune ta rahoto.
Asali: Legit.ng