EFCC: Kotu Ta Fara Zaman Shari'ar Tsohon Ministan da Ake Tuhuma da Kwamushe Dala Biliyan 6

EFCC: Kotu Ta Fara Zaman Shari'ar Tsohon Ministan da Ake Tuhuma da Kwamushe Dala Biliyan 6

  • Tsohon ministan wutar lantarki da karafa, Olu Agunloye na fuskantar shari'a bisa zargin almundahanar dala biliyan 6
  • Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati (EFCC) ta ayyana neman tsohon Ministan ruwa a jallo a watan Disambar 2023
  • Ya samu beli kan Naira miliyan 50 da kuma sanannun mutum 2 waɗanda zasu tsaya masa mazauna Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Rahotanni da ke fitowa sun tabbatar da cewa babbar kotun birnin tarayya Abuja ta fara sauraron shari’ar tsohon ministan wutar lantarki da karafa, Olu Agunloye.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da hukumar yaƙi da rashawa EFCC ta fitar ranar Juma’a, 12 ga watan Janairu, kuma mai shari’a J. O. Onwuegbuzie ne zai jagoranci shari’ar.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta maida martani kan nasarar Gwamna Abba na Kano da wasu gwamnoni a kotun ƙoli

Tsohon ministan wutar lantarki, Agunloye.
Zargin damfarar Dala Biliyan 6: Kotu Ta Fara Shari'ar Tsohon Minista Agunloye Hoto: EFCC
Asali: Twitter

EFCC ta gurfanar da Agunloye gaban ƙuliya ne bisa tuhume-tuhume bakwai masu alaƙa da almundahanar bada kwangila da cin hanci na kuɗin da suka kai dala biliyan 6.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waɗannan tuhume-tuhumen sun ci karo da sashe na 22(4) na kundin dokokin rashawa da sauran laifukan da ke da alaƙa na shekarar 2000.

Yadda kotu ta yi zaman shari'ar

A ranar Alhamis, 11 ga watan Janairu, kotun ta yi zama domin daukar mataki kan bukatar ba da belin tsohon ministan wanda lauyansa, Adeola Adedipe, SAN, ya gabatar.

Sai dai a wannan zama lauyan mai ƙara EFCC, Abba Muhammed, ya yi musun bada belin da kakkausar murya.

Muhammed ya kafa hujjar rashin amincewarsa ne a kan hujjoji guda biyu masu cin karo da juna da aka gabatar domin kotu ta amsa bukatar belin.

Kotu ta bada belin Agunloye kan N50m

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Babbar Kotu ta yanke hukunci kan tsohon ministan da ake zargi da karkatar da $6bn

Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Onwuegbuzie ya amince da bayar da belin Agunloye a kan kudi naira miliyan 50, da mutum biyu sanannu da zasu tsaya masa.

Alkalin ya kafa sharaɗin cewa waɗanda zasu tsaya masa dole su kasance mazauna Abuja kuma zasu gabatar da kwafin katinsu na ɗan ƙasa da fasfo.

Bugu da ƙari, dole Agunloye ya mika takardun farfo ɗinsa ga magatakardar kotu, ba zancen fita kasar ba tare da izinin kotu ba, sannan kotu ta tantance adireshin gidan da yake zaune.

Tinubu ya faɗi gaskiya kan talaucin Najeriya

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa babu dalilin da zai sa Najeriya da mutanen cikinta su zauna cikin talauci.

Shugaban ƙasar ya ce duk da karancin ababen more rayuwa, iimi da kiwon lafiya, ƙasar nan tana da albarka mai tarin yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262