Kaza Mafi Tsufa a Duniya Ta Mutu Cikin Baccinta Tana da Shekaru 21 a Duniya a ranar Kirsimeti
- Wata kaza da ta shafe tsawon shekaru 21 a duniya ta mutu ta bar uwargijiyarta, wacce ta kula da ita tsawon lokaci cikin bakin ciki
- Kazar mai suna Peanut mallakin Marsi Darwin, wata mutuniyar Michigan ne kuma ita ta sanar da labarin mutuwarta a shafinta
- Mahaifiyar Peanut ta yasar da ita, inda Marsi ta kyakyashe ta daga cikin kwanta, sannan ta ajiye tare da kula da ita tsawon shekaru 21
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wata kaza ta mutu tana da shekaru 21 a duniya bayan mai ita ta ajiye tare da kula da ita tun tana yar jinjira.
Sunan shahararriyar kazar Peanut, kuma mallakar wata mutuniyar Michigan ce, wacce ta yi wallafa don jimamin mutuwarta a ranar 25 ga watan Disamba.
Peanut, wacce ta shiga kundin bajinta na duniya wato Guinness World a matsayin kaza mafi tsufa a duniya, ta mutu cikin barcinta a safiyar ranar Kirsimeti.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai kazar ta yi alhinin rashinta
A wallafar tata, mamallakiyar Peanut, Marsi Darwin, ta bayyana yadda kazar ta mutu kuma cewa za ta yi kewar abar kiwon tata.
Ta ce:
"Na shafe daren ranar 23 rike da Peanut, sannan a jajiberin Kirsimeti, cike da gajiya na kai ta gadonta, na lullube ta a cikin bargo mai laushi sannan na kai ta kusa da kirjina. Na ji dan karamin kanta kwance kan kafadata kamar yadda take yi tsawon shekaru, sannan da misalin karfe 5:00 na safe wuyanta ta langwabe a nawa, kuma a nan na san ta mutu cikin lumana a baccinta, kyautarta ta karshe a gareni."
Marsi ta yi alhinin mutuwar kazar da ta shafe shekaru a hannunta tun bayan da mahaifiyarta ta yasar da ita shekaru 21 da suka wuce.
"A yanzu, gajimare ya rataya a daular Darwin. Na wargaza bukkar ta da ke kan kujerar taga, sannan duk lokacin da na tsinci gashinta yayin da nake tsaftace yankinta, yana sa ni hawaye. Duk da cewar akwai mage da akku guda uku, gidan ya koma shiru tamkar ba kowa. Na san ranaku masu haske na zuwa a lokaci. Amma za mu yi kewarta har abada."
Matashi ya yi lalata da zakara
A wani labri na dabn, mun ji cewa rundunar yan sanda ta kama wani matashi dan shekaru 17 mai suna Lawali Mori kan zargin lalata da wani zakara a Viniklang, karamar hukumar Girei ta jihar Adamawa.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki ta shafin rundunar a dandalin X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) @AdamawaPoliceNG, a ranar Juma'a, 8 ga watan Disamba.
Asali: Legit.ng