'Yan Sandan Kaduna Sun Kama Mutane 3 Kan Zargin Satar Kebura
Kaduna - Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wasu mutane uku bisa zargin satar wayar wuta ta alminiyo a garin Saminaka da ke karamar hukumar Lere ta jihar.
Mai magana da yawun rundunar, ASP Mansir Hassan, shi ya bayyana haka ranar Lahadi a Kaduna.
Hassan ya ce da misalin karfe 4:00 na asuba ranar Lahadi, rundunar ta samu rahoton satar wayar wuta a wata karamar unguwa da ke titin Kafanchan, Garin Saminaka, cewa an ga wasu da ba a san ko su waye da wayar wuta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Tawagar sintirinmu sun dira unguwar, kuma sun kama wanda ake zargi su uku da suka fito daga Unguwar Bawa", in ji shi.
Hassan ya ce an kama wanda ake zargin da wayar wuta ta alminiyo da adduna lokacin da aka kama su.
A cewarsa, wanda ake zargin sun amsa laifin yanko wayar wuta daga turakun wuta a titin Saminaka-Kafanchan.
Hassan, ya bayyana cewa tuni aka sanar da lamarin ga kamfanin rarraba wuta na Kaduna, ya ce har yanzu ana ci gaba da bincike.
Ya ce za a tura wanda ake zargin kotu da zarar an kammala bincike
Asali: Legit.ng