Ikon Allah: Abinda Ya Faru a Ofishin Gwamnan Ondo Bayan Samun Labarin Ya Mutu
- Bayan ɓullar labarin rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu, ofishin gwamnan da ke gidan gwamnatin Ondo a Akure ya zama babu kowa
- Rahotanni sun bayyana cewa kowa ya kama gabansa ya bar ofishin sauran jami'an tsaro ƙaɗai da aka bari suna gadi
- Gwamman ya rasu ne bayan fama da doguwar rashin lafiya, ya cika yana da shekara 67 a duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Rahotanni sun bayyana cewa ofishin gwamnan jihar Ondo da ke birnin Akure ya shiga yanayin alhini biyo bayan samun labarin rasuwar Gwamna Oluwarotimi Akeredolu.
A rahoton Leadership, bayan yaɗuwar labarin cikawar Gwamna Akeredolu, gwamnatin jihar Ondo ta yi gum da bakinta a hukumance, lamarin da ya jefa Akure cikin alhini.
Majiyoyi masu ƙarfi daga gidan gwamnatin jihar sun tabbatar da rasuwar Akeredolu amma bisa sharaɗin boye bayanansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da ya faru a ofishin gwamnan Ondo
Rahotanni sun bayyana cewa ofishin gwamna da ke Akure, wanda ya saba cika da jama'a ana tafiyar da harkoki har a washe garin kirsimeti, ya koma ba kowa a yanzu.
Dukkan ma'aikata da hadiman da ke aiki a ofishin sun kama gabansu, jami'an tsaro kaɗai ya rage suna gadin ofishin a yanzu.
An tattaro cewa an kulle kofoshin ofishin gwamnan kuma babu komai a kan tebura yayin da jami'an tsaro suka mamaye ƙofar shiga.
Manyan mutane sun fara tura saƙon ta'aziyya
Tun bayan tabbatar da rasuwar Gwamna Akeredolu, manyan ƙusoshi a ƙasar nan suka fara nuna alhini da kuma ta'aziyyar rasuwar mai girma gwamnan.
The Nation ta ce kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta bakin shugabanta kuma gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ta ce ba za a taɓa mantawa da Gwamna Akeredolu ba.
NGF ta kuma miƙa sakon ta'aziyya ga kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC, gwamnati da al'ummar jihar Ondo, da kuma dangin mariagayi Akeredolu.
Shettima ya dira a jihar Filato
A wani rahoton kuma Sanata Kashim Shettima ya ziyarci jihar Filato domin duba waɗanda hare-haren jajibirin kirsimeti ya shafa a kananan hukumomi 2.
Mataimakin shugaban ƙasar ya samu tarba daga NSA, babban hafsan tsaro, Gwamna da wasu jiga-jigai a jihar.
Asali: Legit.ng