Bidiyon Matashi Yana Fasa Asusun da Ya Shafe Tsawon Shekara 1 Yana Tara Kudi Ya Girgiza Intanet
- Wani mutum ya baje kolin kudaden da ya shafe tsawon shekara guda yana tarawa a cikin asusunsa na katako
- Kamar yadda ya nuna a bidiyon, mutumin yana ta jefa kudade yan KSh 200, 500 da 1000, sannan ya yi su filla-filla kafin ya daure su da roba
- Jama'a sun yaba kokarinsa, yayin da wasu suka ce makudan kudaden da mutane ke tarawa zai fara janyo bata gari gida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wani bidiyo da ke nuno wani mutum da ke fasa asusunsa na katako tare da fito da takardun kudade da suka hada da KSh 1000 da KSh 500 ya ba mutane da dama mamaki.
Yadda wani mutum ya tara dubbai a 2023
Mutumin wanda ba a bayyana sunansa ba ya shiga gasar nan na yan Kenya da ke nuna yawan kudaden da suka tara a gida tsawon shekarar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A bidiyon wanda @mpashogram ya wallafa, an gano mutumin kasar Kenyan yana amfani da wuka don bare asusun, inda a karshe ya fito da gaba daya abun da ke ciki ya baje su kan tabarma.
Abun da ya ba mutane da dama mamaki shine cewa mutumin na ta tara takardun kudi da suka hada da KSh 1000 da KSh 500, kuma har ya gama bai bayyana adadin kudin da ya tara ba a karshe, ya burge mutane da dama.
Daga nan sai ya hada kudin ya daure, bayan ya banbance KSh 500 daga 1000 sannan ya baje sakamakon karshen.
Bidiyon ya kuma nuno wata mata tana fasa goran da ta zuba silallan da take ta tarawa tsawon shekara.
Kalli bidiyon a kasa:
Mutanen Kenya da dama sun bayyana yadda abun ya burge su, yayin da sauran suka yi caa kan masu baje kolin abun da suka tara a shekara.
Ga wasu martani daga masu amfani da soshiyal midiya
_abed_ke ya ce:
"Ka tara kudi don kashewa a Disamba mu muna kashewa a kullun."
omoshricky ya ce:
"Kankan da kansa."
Matashi ya fadi sirrin tara kudi a Canada
A wani labarin kuma, mun ji cewa wani mazaunin New Brunswick ya yi bayanin yadda baki za su iya samun makudan kudade a Canada.
A wani bidiyo mai tsawon mintuna 9 a TikTok, dan Najeriyan ya shawarci jama'a da su daina tura kudi gida don gina masu gidaje.
Asali: Legit.ng