Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Allah Ya Yi Wa Fitaccen Jarumin Shirin Fim Rasuwa
- Fitaccen jarumi a masana'antar shirya fina-finai ta kudancin Najeriya, Nollywood, Dejumo Lewis, ya mutu yana da shekara 80 a duniya
- Jarumi Saidi Balogun ne ya sanar wannan rasuwa ranar Asabar, 23 ga watan Disamba, 2023 a dandalin sada zumunta
- Masoyan marigayi jarumin sun garzaya shafukan sada zumunta suna jimami tare da rubuta kalaman bankwana da mamacin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Shahararren jarumi a masana'antar shirya fina-finan turanci, Nollywood da ke kudancin Najeriya, Dejumo Lewis, ya riga mu gidan gaskiya.
Fitaccen jarumin ya rasu ne yana da shekaru 80 a duniya bayan fama da wata rashin lafiya da ba a bayyana ba kawo yanzu.
Abokin aikinsa a masana'antar shirya fim, jarumi Saidi Balogun, shi ne ya sanar da rasuwar fitaccen jarumin a shafinsa na Intagram.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A sanarwan da ya wallafa yau ranar Asabar, 23 ga watan Disamba, 2023, jarumi Balogun ya rubuta, "Mu kwana lafiya Dejumo Lewis."
Haka nan kuma jarumin ya yi wa mamacin fatan samun salama a rayuwa ta gaba da zai yi a barzahu.
Sai dai har kawo yanzu da muke tattara wannan rahoton, babu wani cikakken bayani kan abin da ya yi sanadin rasuwarsa.
Fina-finan da margayi Lewis ta taka rawa a ciki
Marigayin ya taka rawa da fina-finai da dama kamar irin su, "A place in the Stars," da kuma, "Crossroad."
Bugu da ƙari, Margayi Lewis ya fito a matsayin Sarki, "Oloja na Oja" a kayataccen shirin nan mai dogon zango, "Village Headmaster" wanda aka jima ana haska shi a NTA.
Masoya da masu fatan alheri sun jajanta tare da jimamin wannan rashi a kafafen sada zumunta. Haka nan kuma sun yi masa addu'ar samun salama a bayan mutuwa.
Yan sanda sun ragargaji yan bindiga a Katsina
A wani rahoton na daban Yan bindiga sun ga takansu yayin da dakarun yan sanda suka far musu a yankin ƙaramar hukumar Kankara ta jihar Katsina
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
Asali: Legit.ng