"An Fara Ruwan Kuɗi" Gwamnatin Tinubu Ta Fitar da Sabuwar Sanarwa Kan Biyan Kuɗin N-Power
- Gwamnatin Najeriya ta fara yi wa masu cin gajiyar tsarin Npower ruwan alert na kuɗaɗen da suke bin bashi
- Ministar jin kai da yaƙi da talauci, Dokta Betta Eddu, ta tabbatar wa ƴan Npower cewa kowa zai ga kuɗinsa a asusun banki
- Dokta Edu ta kara da cewa an yi wa tsarin garambawul domin cika burin gwamnatin APC na rage zaman kashe wando a Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayyan Najeriya karkashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta tabbatar da cewa masu jin gajiyar N-Power cewa an fara angiza musu kuɗi yanzu haka.
Wannan na kunshe a wani sakon tabbatarwa da sashin kula da harkokin walwala (NASIMS) ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba.
Nazarin shekara: Shugaba Tinubu da wasu manya jigan-jigan siyasa da suka samu gagarumar nasara a 2023
N-Power: "An fara biyan ƴan C2" NASIMS
NASIMS ya bayyana cewa masu cin gajiyar N-Power na rukunin C2 ne kaɗai aka fara biya hakkokinsu da suka jima suna jira a halin yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakon NASIMS ya ce:
"Ku sani, yayin da ake ci gaba da biyan kuɗaɗen bashi, a yanzu ƴan C2 kaɗai aka fara yi wa alert, ku ci gaba da bibiyar mu."
Bugu da ƙari, ministar jin ƙai da kawar da talauci, Dokta Betta Edu, ta ce biyan bashin N-Power da aka fara daga ranar Laraba, 20 ga watan Disamba, ba zai tsaya ba har sai kowa ya samu.
Eddu ta bayyana haka ne yayin hira da kafar talabijin ta Channels ranar Alhamis da daddare. Ministar ta ce:
"Yanzu haka an fara biyan bashin ƴan N-Power, muna ofis muna aiki jiya har sai da safiyar yau ta tunkaro domin tabbatar da mutanen nan sun samu kuɗinsu da tsohuwar gwamnati ta riƙe masu."
"Saboda haka ina tabbatar muku ƴan N-Power cewa kamar yadda kuka shaida kuɗaɗe sun fara sauka a asusunku, ba zamu tsaya ba har sai na ƙarshe ya samu."
"Kuma muna tabbatar muku da cewa mun yi wa wannan tsarin garambawul domin rage rashin aiki da kuma samar da ayyukan yi ga ƴan Najeriya."
Masu cin gajiyar N-Power sun tabbatar
Ɗaya daga cikin waɗanda suka ji alat na N-Power, Abdulhafiz Tukur, ya shaida wa wakilin Legit Hausa cewa duk da sun ji daɗi amma ba haka suka yi tsammani ba.
Ya ce:
"Eh maganar haka take, ni kaina na samu alat ɗin wata ɗaya N30,000 amma mun yi tsammanin zasu biya ya wuce na wata ɗaya a lokaci ɗaya."
"Mun ji daɗi kasan su kuɗi suna da daɗi, muna nan mun zuba ido mu ga yadda za a biya mu sauran watanni takwas da muke bi bashi."
A ɗaya bangaren kuma wani matashi, Umar Idris, ya faɗa mana cewa shi dai har yau Jumu'a bai ga komai ba kuma yana daga cikin ƴan C2.
"Sun tura ma abokina amma ni har yanzun shiru kake ji, ni ina amfani da Sterling ne amma shi abokin nawa First Bank ne," in ji shi.
FG zata kawo karshen karancin Naira a 2024
A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya ta baiwa ƴan Najeriya haƙuri kan karancin takardun kuɗin da ya dawo sabo a ƴan kwanakin nan.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Muhammed Idris, ya ce matsalar da aka shiga ba da gangan aka kawo ta don kuntata wa mutane ba.
Asali: Legit.ng