“Za a Biya Shi N144m”: An Saki Mutumin da Ya Shafe Shekaru 48 a Kurkuku Bayan An Gano Bai da Laifi

“Za a Biya Shi N144m”: An Saki Mutumin da Ya Shafe Shekaru 48 a Kurkuku Bayan An Gano Bai da Laifi

  • An saki wani mutum da aka aika kurkuku bisa kuskure a 1973 bayan an gano cewa bai da laifi
  • Glynn Simmons ya yi asarar kuruciyarsa a kurkuku bayan an yanke masa hukuncin kisa a 1973
  • Sai dai kuma a 2023, kwakkwaran shaida ya nuna cewa sam bai aikata laifin da aka hukunta shi a kansa ba

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

An sako wani mutum daga gidan yari bayan an tabbatar da bai aikata laifin da aka hukunta shi a kansa ba.

An hukunta mutumin mai suna Glynn Simmons a 1973 kan kisan Carolyn Sue Rogers, amma a kodayaushe ya kan sanar da cewar bai aikata ba.

Wani mutum ya shaki iskar yanci bayan shekaru 48 a kurkuku
“Za a Biya Shi N144m”: An Saki Mutumin da Ya Shafe Shekaru 48 a Kurkuku Bayan An Gano Bai da Laifi Hoto: News 59, Oklahoma KWTV and Doug Hoke/The Oklahoman via AP.
Asali: UGC

Daga karshe a 2023, an sake bitar hukuncin da aka yanke masa, sannan alkali ta sanar da cewar an kulle glynn bisa kuskure.

Kara karanta wannan

Ina za ki damu: Mata ta hada baki da mijinta sun hallaka abokinsa a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mutum ya shaki iskar yanci bayan an hukunta shi bisa kuskure na tsawon shekaru 48

Abun bakin ciki, hakan na zuwa ne shekaru 48 bayan an tura Gynn da wanda aka zargesu tare, Don Robert gidan yari.

Da take yanke hukunci kan karar, Alkalin gundumar Oklahoma Amy Palumbo ta ce:

"Wannan kotu ta gano ta bayyanannun hujjoji masu gamsarwa cewa laifin da aka yankewa Mista Simmons hukunci a kai, tare da daure shi da aka yi... ba Mista Simmons bane ya aikata ba."

Glynn, wanda ke da shekaru 71 a duniya yanzu, yana da shekaru 23 lokacin da aka yanke masa hukuncin kisa a 1973. Daga bisani aka mayar da hukuncin zuwa daurin rai da rai a 1977.

Da yake martani kan sakinsa da aka yi, Glynn ya ce:

"Wannan darasi ne na juriya da jajircewa. Kada ka bari wani ya gaya maka cewa (wanke mutum daga zargi) ba zai iya faruwa ba, domin yana iya faruwa da gaske."

Kara karanta wannan

Bidiyo ya bayyana yayin da alkaliyar Kotun Koli ta kira sanatoci da mijinta yayin tantance ta

Bayan shakar iskar yanci, za a biya Glynn $175,000 a matsayin diyyar daure shi da aka yi bisa kuskure. Yana kuma iya maka Oklahoma City a kotu kan hukunta shi kan laifin da bai aikata ba.

Lauyansa, Joe Norwood, ya ce Glyn na kokarin ci gaba da rayuwa a yanzu. NPR ta nakalto shi yana cewa:

"Dole ne Glynn ya yi rayuwa ba tare da shirin neman tallafi na GoFundMe ba. Haka mutumin yake rayuwa a yanzu haka, yana biyan haya, siyan abinci. Nema masa diyya, da samun diyyan ba tabbass bane, abu ne na gaba kuma dole ya daidaita kansa a yanzu."

Magidanci ya yiwa matarsa yankan rago

A wani labarin, wani magidanci ya caki matarsa sau 15 kafin ya fille mata kai da takobi a kauyen Faljagadh, Uttar Pradesh, Delhi.

Kamar yadda Daily Mail ta rahoto, fusataccen mijin mai suna Dharamveer ya kashe matarsa, Sundari a wani irin yanayi na rashin imani kan ta yi jinkirin hada masa shayin safe a ranar Talata, 19 ga watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng