Hawaye da Tsoro Yayin da Gwamnan APC Ya Tsige Ma’aikata Masu Yawan Gaske

Hawaye da Tsoro Yayin da Gwamnan APC Ya Tsige Ma’aikata Masu Yawan Gaske

  • A yanzu haka ana ci gaba da gyare-gyare a ma'aikatar ruwa ta jihar Lagas idan rahotannin da ke fitowa suka zama gaskiya
  • Legit Hausa ta rahoto cewa kimanin ma'aikata 450 sun rasa ayyukansu, inda za a kuma yi waje da karin wasu
  • Ma'aikatan sun kadu cewa gwamnatin Babajide Sanwo-Olu ta sallami mutane masu yawa haka a cikin kwana daya

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Ikeja, jihar Lagos - Ma'aikatan ma'aikatar ruwa ta jihar Lagas na cikin wani hali a yanzu haka.

Hakan ya faru ne sakamakon sallaman ma'aikata 450 da gwamnatin jihar ta yi.

Gwamnatin Lagas ta sallami ma'aikata
Hawaye da Tsoro Yayin da Gwamnan APC Ya Tsige Ma’aikata Masu Yawan Gaske Hoto: Babajide Sanwo-Olu, Oghara Voice
Asali: Facebook

Ma’aikatan Hukumar Ruwa na Jihar Legas sun rasa aikinsu

Legit Hausa ta samu labarin cewa al'amarin ya afku ne a ranar Alhamis, 30 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Lalong ya magantu kan barin majalisar Tinubu ko komawa majalisar dattawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Punch ta rahoto a ranar Juma'a, 8 ga watan Disamba, cewa ma'aikatan na Lagas da abun ya shafa sun kadu lokacin da aka mika masu takardun sallama daga aiki a ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba.

Lamarin ya sa wasu ma'aikata da abun bai shafa ba sun shiga tashin hankali.

Wani ma'aikaci ya yi bayanin cewa:

"Babu wanda ya san cewa hakan zai faru. Duk mun kadu cewa ana iya sallaman mutane masu yawa haka a cikin kwana daya.
"Abun ya shafi daya daga cikin abokaina. Tana da iyali da take kula da su. Bata ma san daga ina za ta fara ba. Ta bar ofis tana kuka a makon jiya.
"Koda ace za su sallami wani, da ya kamata ace sun ba mutane karin lokaci don su samu mafita."

An fahimci cewa an kori ma'aikatan ruwa na Lagas ne saboda sake fasalin abubuwa da gwamnatin jihar ke ikirarin tana yi. Sai dai kuma, ma'aikatan sun yi korafin karancin ma'aikata.

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna Sani ya caccaki kalaman DHQ kan dalilin jefa bam a taron Musulmai, ya nemi abu 1

Ma'aikatar ruwa ta yi martani

A halin da ake ciki, Kehinde Fashola, kakakin ma'aikatar, ya tabbatar da sallaman aikin. Sai dai kuma, Fashola ya ce ma'aikatan da aka sallama sun take yarjejeniyar daukarsu aikin.

Ya ce:

"Wasun su sun kasance ma'aikatan wucin gadi tsawon shekaru 10 sannan wasun su shekaru biyar, wanda bai yi daidai da dokar kwadago ta kasa ba. A bisa ka'ida shekaru biyu ne."

Gwamnan Kano ya sallami ma'aikata

A wani labarin, mun kawo a baya cewa Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya sallami ma'akata 3,234 saboda daukar su aiki ba bisa ka'ida ba, cewar Daily Trust.

Sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Baffa Bichi shi ya bayyana haka a yau Juma'a 24 ga watan Nuwamba a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: