Kungiyoyin Kwadago Sun Yi Gum Kan Batun Janye Yajin Aiki, Sun Yi Karin Haske Kan Ganawarsu da FG
- Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC na iya janye yajin aikin gama gari da ake yi nan ba da jimawa ba
- Koda dai basu fadi matsayinsu ba a hukumance kan janye yajin aikin, amma shugabannin kwadago sun ce suna bukatar ganawa da mambobinsu kafin bayyana matakinsu na gaba
- Hakan na zuwa ne yayin da NLC da TUC suka gana da tawagar gwamnatin tarayya a ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba
Abuja - Shugabannin kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun yarda su tuntubi mambobinsu kan mafita game da yajin aikin gama gari bayan sun gana da tawagar gwamnatin tarayya a ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba.
Yan kwadago za su tattauna da mambobinsu bayan ganawarsu da FG
Koda dai yan kwadagon sun shiga yajin aiki tun a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba, don zanga-zanga a kan dukan da aka yi wa shugaban NLC, Joe Ajaero a jihar Imo, a ranar 1 ga watan Nuwamba, ganawarsu ta Laraba, ta nuna za a samu maslaha, Daily Trust ta rahoto.
Tawagar gwamnatin tarayya da suka hada da mai ba kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ministan kwadago da daukar ma'aikata, Simon Lalong, sun gana da shugabannin kwadagon a ranar Laraba kan yajin aikin da ke gudana a kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da farko Ribadu ya roki yan kungiyar a kan su janye matakin da suka dauka kan halin da ake ciki, cewa an kama wadanda suka farmaki Ajaero.
Da yake magana a karshen taron, shugaban TUC, Festus Osifo, wanda ya jagoranci sauran shugaannin kwadagon zuwa ofishin NSA, bai bayyana lokacin da za a janye yajin aikin ba, jaridar The Sun ta rahoto.
Osifo ya ce za a kai batutuwan da suka tattauna da jami'an gwamnati gaban kungiyoyinsu sannan za su sanar da halin da ake ciki, jaridar The Cable ta rahoto.
"Da dukkan tabbacin da suka ba mu, da alkawarin da ofishin NSA ya dauka na tafiyar da koma, dukkan tattaunawar da muka yi a nan, akwai bukatar mu mayarwa kungiyoyinmu da sako", in ji Osifo.
Ribadu ya kira taron yan kwadago
A wani labarin, mun ji cewa gwamnatin tarayya ta kira taro da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC domin warware yajin aikin da ake yi a faɗin ƙasar nan.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, taron da aka shirya gudanarwa a yammacin yau Laraba, 15 ga watan Nuwamba, an kira shi ne a ƙarƙashin ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro.
Asali: Legit.ng