Yan Daba Sun Kori Masu Zabe a Bayelsa, Sun Yi Harbe-Harbe

Yan Daba Sun Kori Masu Zabe a Bayelsa, Sun Yi Harbe-Harbe

  • Rahotanni sun bayyana cewa wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun farmaki wasu runfuman zabe a Iajw ta Kudu da Sagbama, a jihar Bayelsa
  • Wannan na zuwa ne yayin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ke gudanar da zaben gwamna a jihar Bayelsa tare da wasu jihohi guda biyu
  • Yan bindigar, sun bude wuta bayan da wasu masu zaben su ka yi yunkurin dakatar da su daga sace kayayyakin zaben, wanda a karshe sai da suka cimma nufin su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Bayelsa - Wasu ‘yan daba sun mamaye rumfunan zabe a kananan hukumomin Ijaw ta Kudu da kuma Sagbama, a jihar Bayelsa, tare da yin awon gaba da kayayyakin zabe.

Kara karanta wannan

Zaben Imo 2023: Fada ya barke yayin da INEC ta fara tattara sakamakon zabe

‘Yan daban sun fara kai farmaki ne a yankin Agorogbene mai lambar akwatin zabe, 6, 7 da 8 a gunduma ta 11, da ke Kudancin Ijaw, inda suka lalata kayayyakin zabe.

Yan daba sun kai farmaki Bayelsa
Yan daban sun yi awo gaba da wasu kayayyakin zabe tare da yin harbi kan mai uwa da wabi Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Yan bangar siyasar, sun fara harbe-harbe da bindiga, a lokacin da wasu daga cikin masu zaben suka yi yunkurin dakatar da su daga satar kayan zaben, a cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, sun mamaye cibiyar yi wa mutane rijista, tare da kwashe kayayyakin zabe na rumfunan zabe biyar daga cikin bakwai da aka ajiye a cibiyar.

A unguwar Ogiadiama, rumfar zabe ta 14 a karamar hukumar Ijaw ta kudu, wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki gundumar, amma jami’an tsaro sun fatattake su.

An Sace Jami'in INEC a Bayelsa

Mun kawo maku rahoton yadda aka yi garkuwa da jami’in sa ido ga jami'an zabe (SPO) na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da aka tura gundumar zabe mai lamba 06 a garin Ossioma da ke karamar hukumar Sagbama, jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Kogi: Yan daba sun kashe mai goyon bayan APC a Anyigba

Jami’in na INEC, an ce an yi garkuwa da shi ne a unguwar Amassoma da ke Kudancin karamar hukumar Ijaw, a lokacin da yake jiran ya hau jirgin ruwa, a wata tashar jirgin da ke yankin.

Rikici ya barke a Bayelsa, jami'an sun nemi mafaka

Wani rahoto da ke fitowa ya tabbatar da barkewar rikici a yankin Agudama-Ekpetiama na jihar Bayelsa.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, lokacin da jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ke kafa tantin su domin fara zabe.

Sai dai a lokacin da faɗa ya barke tsakanin matasan yankin, jami’an INEC sun yi sauri sun koma cikin kwale-kwalen su, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Shugabannin LP sun sauya sheƙa a Bayelsa

A wani labarin, kunji yadda dan takarar zaben gwamnan jihar Bayelsa a karkashin inuwar jam'iyyar Labour Party (LP) Udengs Eradiri, ya samu koma baya ana jajibirin zabe.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Imo 2023: 'Yan sanda sun yi arangama da wakilan jam’iyya, an yi harbe-harbe

Wasu shugabannin jam'iyyar na kananan hukumomi shida sun juya wa Udengs Eradiri baya, inda suka ce sun dauki matakin ne saboda tsame su da shugabancin LP ta yi daga tsarin yakin neman zaɓen gwamnan, Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.